Sojojin Najeriya Sun Kashe Mayakan Kungiyar Boko Haram 33 A Yau Talata

0
25
Sojojin Najeriya Sun Kashe Mayakan Kungiyar Boko Haram 33 A Yau Talata

Rahotanni daga jahar Borno sun tabbatar da cewa sojojin Najeriya sun yi artabu da mayaƙan Boko Haram a yankin ƙaramar hukumar Marte a jihar Borno arewa maso gabashin Najeriya.

Jaridar PRNigeria ta ce sojojin sun yi musayar wuta da ƴan ta’addan a yau Talata yayin da suka ƙaddamar da farmaki domin kakkaɓe mayaƙan na Boko Haram a garuruwan Hausari da Missene da Chikungudu da ke cikin ƙaramar hukumar Marte.

Sai dai jaridar ta ruwaito cewa an kashe sojojin Najeriya biyu yayin da bakwai suka samu rauni.

Amma dakarun na Najeriya sun yi nasarar kwashe mayakan na boko haram su 33 tare da ƙwato bindigogi ƙirar AK47 guda 27 da wasu manyan bindigogi masu harbo jirgin sama guda uku da motocin yaƙi biyu daga hannun mayaƙan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here