GA YADDA ZAKAYI ONLINE TRAINING NA NYIF.

0
50
  • Da farko zaka shiga play store daman Already sun riga ya sun aika maka da link ta shi da zakayi downloading na ZOOM Application,da zakake kallon duk abubuwan da ake yi.
  • Zaka shiga application na zoom domin kayi rijista.
  • Za’a tura maka username da password naka da zaka ringa shiga kana Kallon duk abunda akeyi a Class din

Ana so ka halarci training din sannan akwai karuwa sosai zai amfani ka Kuma idan kana sauraren training din kar ka sauka daga kan wayar, ko kayi call, dan zai mayar da kai baya.

zasu turo maka link da zaka cike attendence form din.Idan kuma basu turo maka a lokacin ba, sai kayi hakuri zasu tura maka ta email daga baya, bayan kwana biyu.Idan ka cike attendance form, daga nan zasu turo maka Certificate ta email dinka.Shike nan, sai kuma batun kudin,zasu aika da sunan ka da lambar dake jikin certificate da duk abin daya shafi ka izuwa Nirsal Microfinance.

Wannan dai shirin ne da shugaba Buhari ya kawo domin taimaka wa matasa daga kan masu shekaru 18 zuwa 35, domin a basu rance su gina kansu, su farfado da sana’o’i domin samun hanyar rayuwa.

Shugaba Buhari ya bayar da Naira biliyan 75 ne akan wannan shirin ta hannun Ministry of Youth And Sports Development, karkashin Ministan Doctor Sunday Dare.

Duk shekara za’a bayar da Naira biliyan 25 ga matasan Nigeriya, kudin zai kare ne a dai dai lokacin da Baba zai sauka a 2023 in sha Allah.

Wanda ba’a tura musu sakon gayyata ba izuwa yin training din nan da suyi hakuri za’a tura musu insha Allahu next week za’a cigaba da turawa mutane abin dasu batch by batch ne Allah yasa kowa ya samu wannan rancen kudin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here