HAƊIN KAN MUTANEN JINGIR ABIN KOYI NE GA ‘YAN NIJERIYA

0
52
HAƊIN KAN MUTANEN JINGIR ABIN KOYI NE GA 'YAN NIJERIYA

Daga Abbas Sadi Jikan Liman, Jingir

Tun bayan da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da mai ba shi shawara kan sha’anin tsaro suka kirayi ‘yan Nijeriya da su tashi tsaye su taimakawa ƙoƙarin da gwamnati da jami’an tsaro ke yi na yaƙi da ta’addaci, masu satar mutane da ‘yan bindiga, su daina nuna musu tsoro da barin su suna ta’annati ba tare da an dakatar da su ba, ta hanyar haɗin kai da kishin ƙasa, ‘yan Nijeriya da dama ke bayyana ra’ayoyi mabambanta, bisa la’akari da ganin yadda talakawa marasa ƙwarewa da makami za su iya tunkarar masu riƙe da muggan makamai, marasa tausayi da imani.

Duk da yadda masu irin wannan tunani ke kashe gwiwar wasu ‘yan Nijeriya, daga tunanin fuskantar masu ta’addaci da makamai, wannan bai hana al’ ummar yankin Jingir da ke Ƙaramar Hukumar Bassa a Jihar Filato tashi tsaye, da cire tsoro a ransu su tunkari wani gungun mutane da ake zargin masu garkuwa da mutane suna karɓar kuɗin fansa ne, da wasu masu fashi da makami da suka addabi yankin ba.

Ga duk wanda ya san hanyar Jingir zuwa Jos ko kuma Jingir zuwa Saminaka a Jihar Kaduna, ya san hanya ce da take fama da ɓatagari masu tare hanya suna yi wa matafiya fashi ko satar mutane suna garkuwa da su a cikin dazuka, musamman ma ranar Lahadi, da ta zama zama Ranar Kasuwa a Jingir, babbar kasuwar da ta haɗe garuruwa da dama dake iyakokin jihohin Filato, Bauchi da Kaduna.

A irin wannan rana ta Lahadi ne 14 ga watan Maris, 2021 wasu masu garkuwa da mutane suka kai hari wani ƙauye kusa da Jingir mai suna Mun-Tsira, inda suka sace wasu mutane uku tare da kashe wani matashi magidanci da ya yi ihun neman taimakon jama’a. Labarin wannan al’amari ya watsu kusan a ko’ina a tsakanin ƙauyukan da ke kewaye da yankin kuma babu shakka ya sanya tsoro da firgici a zukatan jama’a.

Washegari Litinin da rana wasu mazauna ƙauyen Bauɗa da ke kusa da Mun-Tsira suka ga ayarin wasu mutane a kan babura da yawan su ya kai kimanin goma sha bakwai, wannan dandazo da suka gani ya haifar musu da zargi da kokwanto kan gaskiyar mutanen da kuma abin da ya shigar da su yanki, duba da yadda ake labarin irin ɓarnar da ‘yan bindiga ke yi a wasu jihohin Arewa, irin su Zamfara, Katsina, Neja da Kaduna.

Wannan tunani shi ya zaburar da mutanen ƙauyen musamman matasa, Musulmi da Kiristan su, suka haɗa kai suka tunkari inda suka ga waɗannan mutane sun nufa, tare da kiran wasu daga cikin mutanen ƙauyen Mun-Tsira don suma su tashi su tunkari ayarin mutanen da ke nufo ƙauyen su, yayin da su kuma suka bi su a baya, aka sa masu baburan a tsakiya.

Lura da ganin ana bin su a baya, ya sa masu baburan suka nemi mafaka a wata maɓoya da ke cikin daji, su kuma mutanen da ke bin su suka ja tunga a bakin wajen, tare da gayyato wasu mutanen daga ƙauyuka na kusa suka kewaye wajen, suna riƙe da sanduna da gororin su. Sannan aka aika da wasu da suka sanar da jami’an tsaro da ke cikin gari.

Bayanai sun tabbatar da cewa, a wannan waje jama’a suka kwana suna gadin waɗannan mutane don kar su fita su gudu, har zuwa wayewar gari, yayin da tawagar jami’an tsaro suka isa wajen da sanyin asuba suka kutsa kai inda waɗannan mutane da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suke ɓoye, aka fitar da su tare da bindigogin da aka ce an samu a tare da su.

Wannan al’amari ya ƙara haɗa kan jama’a a yankin sosai, ganin yadda aka kawar da duk wasu bambance bambance aka tunkari wannan matsala da ake ganin za ta iya jefa yankin cikin babbar damuwar tsaro. Ko da yake ba a rasa wasu da ke nuna fargabar yiwuwar samun ramukon gayya daga ‘yan uwan waɗannan mutane da ake zargin ɓatagari ne ba.

Abin da ya faru ya sake ƙarfafa wa mutane gwiwa sosai da cire musu tsoro a zukatan su, don haka ne ma ranar Laraba 17 ga watan Maris, da aka samu wasu ‘yan fashi da makami su uku da suka far wa wani ɗan kasuwa a cikin garin Jingir, mutane ba su yi wata wata ba suka fatattaki ‘yan fashin da suka ranta a na kare. Ko da yake ba a samu nasarar kama su duka ba, amma an cimma ɗaya daga cikin su, wanda ya gamu da fushin ‘yan Nijeriya, saboda gajiya da halin taɓarɓarewar tsaro da ƙasar nan ke ciki.

Yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da gudanar da bincike game da waɗannan ɓatagari da aka kama, ya zama dole a ƙara jinjinawa jaruman matasan Jingir da kewaye, bisa haɗin kan da suka nuna da jajircewa wajen tallafawa jami’an tsaro da ‘yan sa-kai wajen kare yankin su.

A ƙarshe muna kira ga jama’ar yankin mu na Arewa da ma Nijeriya baki ɗaya, su haɗa kansu su kawar da siyasa da bambance bambancen da ke tsakanin su, don taimakawa ƙasar mu ta samu cigaba.

Abbas Sadi Jikan Liman, Shugaban Ƙungiyar Arewa Media Writers reshen ƙaramar hukumar Bassa a Jihar Filato.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here