Dalilin da ya jawo sararin samaniyar Masallacin Ka’aba ya canja kala(ja jazur)

Ansami Bidiyo wanda ya yaɗu kamar wutar daji musamman a shafin sada zumunta na facebook da Whatsapp, ya sa mutane da dama sun yi amanna cewa “Alamu ne na Tashin Alƙiyama.” A saƙon da ke tafe da bidiyon an rubuta cewa: … (wannan ne abin da ya faru a Saudiyya a yau, iska mai tafe da guguwar rairayin hamada mai launin ja ta rufe sararin samaniyar Masallacin Harami da kewaye.)

Ganin yadda mutane da dama dake ci gaba da yaɗa al’amarin wasu daga cikin hukumar yada labarai sun tuntubi hukumomin da ke kula da Masallatai Biyu Masu Daraja na Saudiyya wato Haramain Sharifain ta shafin yada zumunta wato (twitter), kuma sun yi bayani kan yadda al’amarin ya kasance.

Haramain Sharifain ya ce irin wannan al’amari ya sha faruwa ba ma a Masallacin Ka’aba ba kawai har ma da sauran yankunan ƙasar.

Lamarin yana faruwa ne a duk lokacin da iska ta taso daga Hamadar Sahara mai ɗauke da ƙura.A duk lokacin da irin wannan iska ta taso ta kan turnuƙe sararin samaniyar yankunan ƙasar ta inda ko tafin hannu ba a iya gani.Hukumar Haramain Sharifain ta sake cewa a irin waɗannan lokuta mutane kan ɗauki bidiyo su yi ta yaɗawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *