yadda aka fara amfani da takunkumi a duniya

An daɗe ana saka abin rufe fuska wato takunkumi tsawon shekaru 500 da suka gabata abisa dalilai dayawa.

Koda yake takunkumin fuska na farko ana amfani da shi ne domin ɓoye kamanni ko kuma domin kariya (maimakon wanda ake amfani da shi domin ado) tun a kusan ƙarni na shifa kafin bayyana Annabi Isa (AS).

A baya  an samu hotunan mutane sanye da kyalle a bakinsu a bakin kofar ƙaburɓuran Daular Farisa

A cewar Marco Polo, bayi a ƙarni na 13 suna rufe fuskokinsu da wani abin saƙa. Dalilin shi ne sarki a lokacin ba ya son numfashinsu ya shafi abincinsa ko ɗanɗaɗonsa.

ANNOBA

Black Death Quarantine: How Did We Try To Contain The Deadly Disease? -  HistoryExtra


Cutar da ake kira ‘Black Death’ – annobar da ta ɓarke a Turai a cikin ƙarni na 14, inda ta kashe aƙalla mutane miliyan 25 tsakanin 1347 zuwa 1351 – ya haifar da saka abin rufe fuska. Masana sun yi imanin cewa annobar ta yaɗu ne ta hanyar gurɓataccen iska, wanda ke haifar da illa ga jikin ɗan adam. Sun yi ƙoƙarin toshe kafar da za su shaƙi iskar mai guba ta hanyar rufe fuska.

 takunkumi mai kamar bakin tsuntsu kamar hankaka, bai bayyana ba har sai zuwa ƙarshen annobar wauraren tsakiyar ƙarni na 17.An kuma yi amfani da turare da kayan kamshi – da kuma wani ganye da ake amfani da shi domin kariya daga kamuwa da cutar da ake kira “miasma.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *