ILIMIN SANIN MAGANI A HAUSANCE WALLAFA TA BIYU

0
15

A wannan gaba zamuyi bayani akan kashe kashe magani, zamu fara daga na farko kamar yadda muka bayyana a wallafawar mu ta farko.

KARANTA: ILIMIN SANIN MAGANI A HAUSANCE WALLAFAR FARKO

Maganin da saida umarni likita ake badashi.

MENENE WANNAN MAGANI.

Wannan maganin shine maganin da a dokance aka yadda a bayar dashi a dakin magani

MENENE DALILIN BADA WANNAN MAGANIN SAIDA RUBUTUN LIKITA

Dalilin shine, wannan maganin yana dauke da wani sinadari da zai iya cutar da rayuwar dan adam indai yana amfani dashi ba tare da likita ya rubuta masa ba.

WANNE MAGANI NE YAKE BUKATAR RUBUTUN LIKITA

1. Maganin dauke zafin ciwo ko radadi.(opioid)
2. Maganin dake kashi kwayoyin halittu masu cutarwa.(Antibiotics)
3. Maganin da suke yaye damuwa da kuma tunani.(CNS/PSYCHOTIC)
4. maganin kara kuzari da karfi(stimulants).

BAYANI A KANSU

Maganin dauke zafin ciwo ko radadi.(opioid)

Tun farkon alif 1990s likitoci suka fara rubuta manyan maganin dauke zafin ciwo ko radadi, wadannan sun hada da codeine, hydrocodeine, morphine, da kuma oxycodeine. Wadannan magunguna suna dauke zafin ciwo da sauri duk yawansa sannan yana inganta lafiyar mara lafiya indai yana amfani dashi yadda likita ya rubuta masa.

Amma idan mutum yana amfani dashi ba da umarnin likita ba to zai cutar da rayuwar sa. Sannan yawancin mutanan da suke amfani da wannan magani babu ka’ida zasu iya kamuwa da cuta mai karya garkuwar jiki da kuma cutar hanta.

Maganin dake kashi kwayoyin halittu masu cutarwa.(Antibiotics)

likitoci suna rubuta wannan rukunin magani masu kashe kwayoyin halittu masu cutarwa dan gudun kada a sami bijirewar jiki ga magani (DRUGS RESISTANCE).

Maganin da suke yaye damuwa da kuma tunani.(CNS/PSYCHOTIC)

Likitocin suna amfani da rukunin wadannan magunguna wajen magance damuwa, rashin bacci, da kuma kasayin bacci. Su kuma wadannan magunguna suna yakar sinadarin da yake a kwakwalwar mai suna GABA, shi wannan sinadari yana yana rage aikin kwakwalwa ya kuma saka jiki yayi nauyi sai kuma bacci ya samu.

Sun kunshi, BENZODIAZAPINE, BARBITURATES, PHENOLBARBITOL.

Amfani dasu da sinadarin giya zai iya karancin numfashi haka kuma zai kai ga mutuwa.

Maganin kara kuzari da karfi(stimulants).

Likitoci suna rubuta rukunin maganin nan dan maganin kiba da toshwar numbashi saboda suna kara saurin bugun zuciya, da kara yawan sikari a cikin jini, da karfin gudun jini da kuma bedewar iska.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here