Sako zuwa ga musulman duniya.

0
11

Babban Malamin Musulunci a Nigeria Sheikh Bashir Ahmad Sani Sokoto ya rubuta wani gagarumin Littafi akan kimiyya da Musulunci wanda a wannan karnin wani ‘dan-adam bai taba daukar alkalami ya rubuta irinsa ba.

Sheikh Bashir Ahmad Sani Sokoto Malami ne wanda Allah Ya masa baiwa da sanin ilmin kimiyya da Qur’ani da Hadisi, ni dai yanzu a Nigeria idan akwai wanda ya kaishi bincike akan kimiyya da Musulunci to ban sani ba, ‘yan uwa Musulmi da suke tare dani a WhatsApp da Telegram zasu zama shaida.

Ina yawan fadin cewa tun bayan da Malam Albaniy Zaria ya bar duniya ban hadu da wani Malami da yake tsananta bincike wajen zakulo makircin yahudawan duniya ba akan Musulmi yana bayyanawa kamar Malam Bashir ba, yana bayyana gaskiyar ilimi akan kimiyya da makirce makircen yahudawa ba tare da tsoro ba.

A halin da ake ciki Malam Bashir yana fama da rashin lafiya, amma yayi wani gagarumin aiki ga Musulunci wanda yake fatan ya amfani dukkan Musulmi, ya kuma zama shiriya ga wadanda ba Musulmi ba koda ya bar duniya, kuma Littafin zai taimaki Malaman addinin Musulunci da suke bincike akan ilimi.

A tsawon shekaru sama da 20 da Malam ya share yana karantar da al’ummah, Malam yace bai san wani aiki mai girma da ya barwa Musulunci ba kamar rubuta wannan littafin.

Littafi ne wanda aka samu wasu daga cikin wadanda ba Musulmai ba suka Musulunta ta dalilin karanta littafin tun kafin a buga shi.

Littafi ne wanda yake dauke da tarihin duniya tun farkon ta har karshen ta, da bayanin kimiyyar sarararin samaniya, da na karkashin kasa da kuma teku, da tarihin Dujal, Yajuju da Majuju, da sauran abubuwa masu ban mamaki wanda suke a cikin ilmin kimiyya da Musulunci.

Aikin buga Littafin zai ci kudi mai yawa, kuma ga matsala na rashin lafiya dake damun Malam, Malam yace ya taba adana Littafin akan Laptop ya manta a Saudiyyah, dole ya sake rubutawa, sannan akwai wata Laptop din, itama aka manta password dinta, yanzu dai ya sake tattara littafin, yana so ya wallafa kafin rayuwa tayi halinta

Malam yace bai da halin daukar nauyin buga Littafin wanda yake volume biyu ne, don haka ya fitar da sanarwa ga ‘yan uwa Musulmi su taimaka da kudi domin a samu damar buga Littafin

Duk wanda zai taimaka da kudi to za’a tura kudin ta asusun ajiyar kudi na Malam ne kamar haka

👉🏿Acc Number: 0736223634
👉🏿Acc Name: Bashir Sani Ahmad
👉🏿Bank: Access Bank

Akwai bidiyo da audio wanda Malam yayi cikakken bayani akan Littafin, zan tura a group na WhatsApp da Telegram Insha Allah.

Don Allah ‘yan uwa Musulmi mu taimaka da kudi komin karancinsa, muna fatan abinda zamu taimaka wajen buga Littafin ya zama sadaka da zata amfanemu har zuwa ranar da Allah Zai tashi duniya.

Allah Madaukakin Sarki Ya bamu ikon taimakawa Amin🙏

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here