Nan take alqali farfesa salisu shehu ya yanke hukuncin maqabalar Abduljabbar da malaman kano.

0
13

Malam Abduljabbar ‘ya kasa amsa dukkanin tambayoyin da aka yi masa’

Alkalin muƙabalar a tsakanin
Malam Abduljabbar da malaman Kano ya ce Abduljabbar ya kasa amsa dukkanin tambayoyin da aka yi masa a zaman da akayi na yau.

Alƙalin muƙabalar Farfesa Salisu Shehu shugaban cibiyar addinin Islama da tattaunawa tsakanin addinai ta Jami’ar Bayero(BUK) ya ce “bisa muƙabalar da aka yi Abduljabbar ya cakuɗa bayanansa, kuma wasunsu ba a kan doron ilimin hadisi yake gina su ba.”

“Na yanke hukunci:
Malam Abduljabbar bai bayar da amsoshin tambayoyin da waɗannan malamai suka yi masa ba,” in ji alƙalin muhawarar”(farfesa salisu shehu).

Ya ƙara da cewa babu wata tambaya ɗaya da Abduljabbar ya tunkare ta ya bayar da amsarta.

Kuma ba ya tsayawa kan tambayoyin da aka gabatar masa.

Alƙalin muhawarar ya ce yanzu ya rage ga gwamnati ta yi nazari kan matakin da za ta ɗauka bisa muƙabalar da aka gudanar a yau tsakanin Abduljabbar naseer kabara da wasu daga cikin malaman kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here