Sunayen malaman da xasu gabatar da muqabala a yau tare da Abduljabbar nasir kabara.

0
20

Gwamnatin jihar Kano ba ta bayyana sunayen malaman da za su fafata da Sheikh Abduljabbar nasiru Kabara ba a wannan muƙabalar da za’a gudanar a yau asabar.

Kwamishinan Al’amuran Addini na jihar kano Malam Muhammad Tahar Adamu (Baba Impossible) ya ce sai a wajen muƙabalar ne za a fadi sunayen malaman da za su yi muqabalar.

Haka kuma a baya, ita ma haɗakar malaman ta Kano ta ce ta shaida wa gwamnati malaman da za su wakilce ta, amma ta ce ba za ta bayyana sunayen malaman ba sai a zauren muƙabalar.

Sai dai sanannen abu ne cewa malamai daga ɓangarorin Ahlussunnah da Izala da Tijjaniya da Kadiriyya ne suke ƙalubalantar Sheikh Abduljabbar. Nasir kabara a jahar ta kano.

Wakilin Malaman Ahlussunnah shi ne Sheikh Abdulwahhab Abdullah, sai Shehi-Shehi da ke wakilatar ɓangaren Tijjaniyya, sannan sai Sheikh Ƙaribullah Nasiru Kabara da ke wakiltar ɓangaren Ƙadiriyya, wanda yaya ne ga Sheikh Abduljabbar, yayin da Sheikh Abdullahi Pakistan yake wakiltar ɓangaren Izala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here