Auwal Isah West ya saki sabon video yana bawa Hadiza Gabon haquri akan abinda ya fada a baya.

Jarumin Kannywood Auwal Isah West ya fito ya bai wa abokiyar sana’arsa, Hadiza Gabon hakuri kan raddi da yayi mata

Auwal dai ya caccaki Gabon ne kan shagube da tayi wa wasu manyan jaruman masana’antar da suka yi hotuna da gwarzon cin gasar BBNaija

Ya ce duk abubuwan da ya fadi a baya kan Gabon ya fade su ne bisa bacin rai da zafin zuciya

Shahararren jarumin Kannywood, Auwal Isah West ya fito ya bawa abokiyar sana’arsa, Hadiza Gabon hakuri kan martanin da yayi mata sakamakon caccakar wasu manyan jaruman masana’antar da tayi.

Hadiza dai tayi wani rubutu a shafinta na Instagram inda tayi shagube ga wasu manyan jarumai da daraktocin masana’antar da suka halarci wani gagarumin taro da kamfanin Multi-choice ta shiryawa wadanda suka lashe gasar BBNaija.

Hotunan manyan gwarazan jaruman Kannywood irin su Ali Nuhu, Adam A Zango, Naziru dan Hajiya, Bashir Mai Shadda, Rashida Mai Sa’a, Abba El-mustapha da dai sauransu yayi ta yawo a kafafen sadarwa tare da gwarzon BBNaija, wanda aka sani da White Money.

Sai dai a wallafawar da tayi a shafin nata, Jaruma Hadiza Gabon ta zarge su da shish-shigi inda tace “ko saka hotunan dasukayi gwarzon gasar bai yi ba a shafinsa. Tana nufin White-Money ko saka hotunan beyi ba a shafinsa na Instagram kodan ya nuna irin dadin da yaji. Amma su shish-shigi ya sakasu se yadawa suke a shafikansu na Instagram da kuma sauransu.

Wannan ya saka Jarumin Auwal Isah West ya harzuqa inda har yayi mata wani sharhi da cewa wadannan mutane da take Magana a kai sune suka daukaka ta har duniya ta santa. Lokacin da tazo Nigeria ko hausa bataji tana binsu tana shish-shige musu hakan har yasa suka dauketa suka sakata cikinsu harta fara haska wasu shahararrun fina-finai a masana’antar ta Kannywood wanda ya saka gashi Jarumar me suna Hadiza Gabon har tayi suna ta daukaka a duniya kowa ya santa amma saboda butulci ta iya budar baki zatayi musu rashin kunya.

Kuma a cikin wadanda tayiwa wannan batu cikinsu harda wadanda suka temaka mata tayi suna a duniya amma saboda butulci irin nata gashi ya saka jarumar harta manta da hakan.

Sai dai kuma a wani bidiyo da shafin Gaskiyazalla na Instagram ya wallafa a Instagram, An gano jarumin Auwal Isah West yana bai wa jarumar tare da iyayen da kuma sauran masoyanta hakuri a kan furucin da yayi a baya, yana mai cewa bacin rai ne yasa ya fadi abun da ya fada.

Duk da daii cewa video din da shafin na Gaskiya zalla wallafa ya nuna kamar Jarumin wato Auwal Isah West agaban hukuma yake, wanda hakan y bayyanawa duniya cewar ita Jarumar wato Hadiza Gabon ta fishi daurin gindi yasa harta saka hukuma suka kamashi kuma aka tilasta masa da cewa seya fito Social media ya bayyanawa duniya cewa abinda ya fada qarya yake wanda hakan beyiwa mabiya bayan jarumin dadii ba.

Sannan kkuma hakan ya nuna cewa koda kuwa ace baka da gaskiya a yanxu yanxu indaii har kanada Naira to zata iya siya maka komai a kasarnan.

Ya ce:

Salamu alaikum, sunana Auwal Isah West. Duk abubuwan da na fada a kan Hadiza Gabon na bakar kalma da na fada na zancen kawalinta, ni ban san wannan maganar ba bacin rai shi ya kawo haka yasa harna fadi wadannan maganganun marasa dadi, amma ina mai bawa iyayenta hakuri da yan uwanta da masoyanta sannan da kuma ita kanta, nayi ba daidai ba nayi mata kuskure halin zuciya ce amma dan Allah dan Annabi tayi hakuri, nagode.

Ga bidiyon a kasa:

Wannan shine bidiyon da aka tirsasa jarumin yayi

A baya mun kawo cewa Auwal Isah West ya caccaki abokiyar sana’arsa, Hadiza Gabon bayan tayi hannunka mai sanda ga wasunsu da suka halarci taro da kamfanin Multi-choice ya shirya.

Kamfanin dai ya shirya taron liyafar ne saboda karrama wadanda suka lashe gasar BBNaija a garin Kano, inda manya-manyan jaruman Kannywood irin su Ali Nuhu, Rasheeda mai Sa’a, darakta Bashir Mai Shadda, Naziru Danhajiya, Abba El-mustapha da sauransu suka halarta.

Sai dai kuma, Jaruma Hadiza Gabon ta caccaki abokan sana’arta da yiwa Whitemoney wanda ya lashe gasar shish-shigi. Sannan tace duk rawar jikin da suka dunga yi bai dora su a shafinsa na social media ba.

THANK YOU FOR VISITING OUR SITE.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *