News

An harbi Halyna ta mutu wajen shirin wani film a yau

Wata jarumar film din America me suna Halyna ta mutu sannan kuma wani mutum guda shima kuma ya jikkata bayan da jarumi Alec Baldwin ya harba bindiga ba tare da saninsa ba a wajen daukar wani sabon film da ake dauka a jihar New Mexico dake yankin America.

Jami’an ‘yan sanda na Amurka sun ce Mista Baldwin ya yi harbin ne lokacin da ake daukar fim din ba tare da saninsa ba wanda shima babban jarumin ya furta hakan da cewa tsautsayine da baya wuce rana kuma ya bayyanawa jami’an’ yan sandan da cewa beji dadin rasuwar jaruma Halyna Hutchins ba.

Jarumar mai suna Halyna Hutshins, an garzaya da ita aisibiti a jirgi amma ta mutu sanadin raunukan da ta ji. Sai kuma daraktan shirin Joel Souza wanda ke kwance a bangaren kulawar gaggawa.

Kakakin Mista Baldwin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa harba bindigar da akayi cikin shirinne aka yishi ba daidai ba.

Halyna Hutchins mai shekara 42 na cikin tawagar mutanen da ke lura da hotuna a cikin shirin. Shi kuma Souza mai shekara 48 an dauke shi ne a motar asibiti wato ambulance kai tsaye izuwa asibiti, sai dai har yanzu ba a bayyana halin da yake ciki ba.

Sai dai har yanzu ‘yan sanda na gudanar da bincike kan lamarin da ya faru a Bonanza Creek Ranch, wani fitaccen wuri ne da ake yawan daukar fim a wurin a Qasashen turai.

Cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na AFP ta fitar a yau, ya ce Mista Baldwin ya yi magana da masu bincike.

“A radin kansa ya tattauna da masu binciken a cikin ginin da suke bayan ya gama kuma ya kama gabansa,” in ji kakakinsa.

Kamar yadda yake a bayananta na shafukan sada zumunta Halyna Hutshins ‘yar qasar Ukraine ce kuma ta tashi a sansanin sojin Soviet da ke Arctic Circle.

Ta karanta aikin jarida a birnin Kyiv, da kuma Fim a Los Angeles wato America, a kuma shekara ta 2019 mujallar Amurka ta Cinematographer ta bayyana sunanta a matsayin matashiyar da take haskakawa.

Ita ce daraktar daukar hotuna ta fim din Archenem a 2020, wanda Adam Egypt Mortimer ya ba da umarni.

“Ban ji dadin mutuwar Halyna ba,” in ji Adam Egypt Mortimer.

I’m so sad about losing Halyna. And so infuriated that this could happen on a set. She was a brilliant talent who was absolutely committed to art and to film.

A wata sanarwa da kungiyar shirya fina-finai ta duniya ta fitar ta ce mutuwar babban jarumar me tace hotuna mai suna Halyna Hutchins tayi matukar kada su sosaii duba da yanda take bada gudun mawa sosaii, kuma sun bayyana hakan da babban rashi ne a garesu dama duniya baki daya.

in ji shugaban kungiyar John Lindley da kuma daraktarta Rebecca Rhine.

“Har yanzu babu wasu rubutattaun bayanai akan wannan al’amarin, amma abubuwa za su bayyana nan ba da jimawa ba kadan, kuma muna goyon bayan a gudanar da cikakken bincike kan wannan lamari,”

Mista Baldwin shi ne wanda ya dauki nauyin shirin, kuma ya dauki shirin fim dinne saboda, wani dan shekara 13 wanda jikansa ne da baya jin magana wannan ya janyo kisan tsau-tsain da aka samu na jaruma Halyna Hutchins.

Duka sauran ‘yan uwansa hudu jarumai ne, Baldwin ya fito a fina-finan talabijin masu yawa sosai inda ya taka rawa daban daban tun daga shekarar 1980,

Ya lashe kyaututtuka da dama a matsayinsa na Jack Donaghy a wani fim din NBC 30 Rocks. Kuma kwaikwayon da yake yi akan Donald Trump ya kara daukaka shi tare da samun kyautuka masu yawa, ciki har da ta Emmy wadda ya ci a karo na uku.

Irin wannan lamarin kisan a wajen daukar fim abu ne da bai fiye faruwa ba gaskiya, ba a fiye jin sa bama gaba daya.

Akan yi amfani da makaman gaskiya a yayin daukar fina-finai, kuma ana sanya musu harsashi tamkar na gaske – domin yarika kara kamar kai kace abin yana faruwa ne a gaske.

A cikin shekara ta dubu daya da dari tara da casa’in da uku 1993, Barndo Lee – mai shekara 28 wanda da ne a wajen jarumi Bruce Lee– shi ma ya mutu a lokacin da ake daukar wani fim wanda akewa take da suna The Crown, inda aka yi irin wannan harbi na tsautsayi kuma ya mutu shima nan take ba tare da ankai shi izuwa ga jami’an lafiya na asibiti ba.

WANNAN SHI AKE KIRA DA BANJI BA KUMA BAN GANI BA SEDAII DUK SANDA LOKACI YAYI KAWAII ANA TAFIYA NE INDA YAFI CANCANTA DAKAI.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button