News

Chelsea taci Norwich City 7-0 Mount ya ci kwallaye uku.

Mason Mount ya ci kwallaye uku daga cikin kwallayen da aka jefawa Norwich City, inda Chelsea da ke jagorancin Premier league ta lallasa wa Norwich City jiki a Stamford Bridge.

Tun ana cikin mintina na goma sha takwas ne 18 da take wasan Thomas Tuchel, Mount da Callum Hudson-Odoi suka ci ƙwallo biyu, yayin da Mount ya taimakawa Reece James shima dake Chelsea ya jefawa Norwich City kwallo ta uku kafin zuwa hutun rabin lokaci (half-time).

Dan wasan baya na kungiyar ta Chelsea me suna Ben Chilwell shine shima haziqin fasihin dan wasan daya sake jefawa Norwich City kwallo ta hudu kafin Mount ya sake cin ƙwallaye biyu daga cikin bakwan.

An bawa ɗan wasan baya na Norwich City Ben Gibson jan kati (red card) ya fita daga wasan bayan ya samu katin gargadi guda biyu (yellow card).

Sakamakon wasan ya ƙara jagulawa Norwich City lissafi inda ta ci gaba da zama a ƙasan teburin Premier.

Chelsea ta yi wasan ne ba tare da shararrun ‘yan wasanta guda biyu ba Lukaku da kuma Werner waɗanda ke jinyar raunin da akayi musu a wasansu daya gabata, yayin da Tuchel ya yi amfani da Kai Havertz da kuma Mount da Hudson-Odoi.

Yanzu haka qungiyar ta Chelsea tana da maki 22 a saman teburin Premier, tazarar maki 4 ne tsakaninta da Liverpool da ke shirin haduwa da Manchester United a Old Trafford.

Wasu kungiyoyin da ke buga gasa a MIDLANDS sun kafa tarihin cin kwallo arba’in da 44 a bugun daga kai sai mai tsaron raga wato penalty a Ingila.

Tarihin da ake da shi a baya shine na cin kwallo talayim da hudu 34 da aka yi a wasa tsakanin matasan Chelsea ‘yan kasa da shekara 23 da Oxford United a gasar EFL Trophy.

Na biyun kuwa shine tsakanin Taunton Town da kuma Truro City a gasar Kudanci ta Challenge Cup da aka ci fenariti 34 a karawar.

Sai wannan karawar ta Old Wulfrunians daga Wolverhampton da Lane Head daga Bloxwich da suka kafa sabon tarihi a wannan season din.

Tun farko sun tashi 3-3 a gasar JW Hunt Cup zagayen farko daga nan ta kai ga bugun daga kai sai mai tsaron raga wato fanareti da Old Wulfs ta yi nasara da ci 19-18 wato kwallo 44 kenan suka buga jumulla.

An fara buga gasar JW Hunt Cup tun daga 1926 har ila yau.

Shahararren Dan wasan Manchester United, Cristiano Ronaldo ya ce yana da tabbacin cewar kungiyar Old Trafford na bukatar lokaci, kafin ta koma kan ganiyarta a bana.

Manchester United tana a matsayin ta shida nd a teburin Premier League da tazarar maki biyar 5 tsakaninta da Chelsea mai jan ragama a yanxu. bayan da ta hada maki daya a wasa uku baya a gasar.

Kungiyar da Ole Gunnar Solskjaer ke jan ragama za ta karbi baquncin Liverpool wadda keda maki kwaya goma tsa takwas 18 a matsayi na biyu a Premier league da za su kara a Old Trafford ranar Lahadi.

”Muna cikin wani yanayi a ra’ayina da cewar Manchester United na bukatar dan sauye-sauye” in ji kyaftin din tawagar Portugal mai shekara 36.

”Sun sayo ni da Raphael da Jadon Sancho, lokaci kadan za mu koma kan ganiya”

Kafin fara kakar bana ta wannan shekarar, United ta dauko dan kwallon Portugal daga Juventus, sannan ta sayo mai tsaron bayan Real Madrid, Varane da kuma Sancho daga Borussia Dortmund.

Cristiano Ronaldo ne ya ci wa Manchester United kwallo na uku a Champions League, bayan da Atalanta ta ci biyu aka farke aka doka ta 3-2 a tsakiyar mako.

Kawo har izuwa yanzu Ronaldo ya ci kwallo shida 6 a wasa takwas 8 da ya yi wa Qungiyar Manchester United a bana.

THANK YOU FOR VISITING OUR SITE.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button