Health

Yadda mata ke iya adana ƙwayayen haihuwarsu zuwa wani lokaci.

A yau a faɗin duniya, da yawa yawan mata da dama sun fara ɗaukar matakin adana ƙwayayensu na haihuwa don gudun wucewar lokacin da jikinsu zai rika samar da ƙwan ma’ana su jinkirta haihuwa kuma su kasa ɗaukar ciki.

Akan cire ƙwayayen daga jikin mace mafi akasari sai a daskarar da su sannan idan ta shirya ɗaukar ciki a fito da su ma’ana a tayar dasu su tashi suci gaba da aiki daga inda suka tsaya, su saki sannan a yi mata dashensu a mahaifarta domin taci gaba da haihuwa wanda yawancin hakan yafi faruwane ga mata ‘yan boko masu karatu wadanda basason su samu haihuwa ya riskesu yayin gudanar da karatunsu saboda kada haihuwar ta janyo musu matsala fagen karatun nasu.

Damar mace ta ɗaukar ciki na raguwane yayin da take ƙara tsufa saboda inganci da yawan ƙwayayen halittarta suma suna raguwane kamar yanda kwari da kwaliti na jikinta suma suke raguwa.

Daskarar da ƙwayayen na jikin mace wani yunƙuri ne hakan na adana wata damarta ta haihuwa ta hanyar daskarar da ƙwan a lokacin da mace take da kuriciyarta kuma ƙwayayenta ke da inganci sosai a wannan lokacin.

Shin yaya ake daskarar da ƙwayayen ?

Da farko, za a fara yi wa mace gwaji wato test domin a tabbatar ba ta ɗauke da wata cuta kamar irinsu HIV (cutar qanjamau) ko kuma ciwon hanta na (Hepatitis).

Yin gwajin ba zai shafi yiwuwar daskarar da ƙwan ko rashinsa ba, koda anyi gwajin ko kuma ba’ayi ba lalle akwai yiwuwar daskarar da kwan yin gwajin kawai yana da alaqa ne da son anaso don a tabbatar an ware ƙwan ko kuma kwayayen da cutar ta shafa daga sauran lafiyayyu saboda idan ba’a ware suba zasu shafawa sauran wadanda suke lafiya kalau.

Daga nan kuma sai a fara bin matakan inganta ƙwayayen, wanda wannan kan ɗauki mako biyu zuwa uku kuma a kan bai wa mace magungunan da za su ƙara yawan ƙwayayenta kuma su taimaka musu su riƙa sosai. Daga nan kuma sai a ciro su daga jikin macen bayan an yi mata allurar bacci.

Bayan ciro ƙwan ana zuba shi a cikin wani sinadari domin a adana shi kuma a kare shi daga abubuwan da kan iya yi masa illa nan gaba.

Daga nan sai a daskarar da ƙwan ta hanyar sanyaya su sannan a zuba su a cikin wani wuri mai cike da sinadarin ruwan nitrogen me sanyi da iska bame cutarwa ba.

Ana iya adana su tsawon shekaru goma wanda bayan nan kuma idan suka haura shekaru goman ba za’a iya amfani da su ba wajen yin dashe, sai dai a zubar dasu saboda sun haura qa’idar tsawon lokacin da suke dauka a waje.

Idan mace ta yanke shawarar ɗaukar ciki ta hanyar amfani da ƙwayayenta da aka adana mata, sai a ciro su daga ma’adanarsu a bari su sake riqa sannan a ƙyanƙyashen ƙwan a ɗakin gwaji, daga nan sai a dasa mata ɗan tayin a mahaifarta bayan ya gama zama mutum kuma shikenan daganan kuma seta haifi jaririnta ko kuma jaririryarta.

Shin wai menene ya saka ake adana ƙwan mace?

Daskarar da ƙwai zaɓi ne ga matan da ba su shirya haihuwa ba a gaɓar da suke amma suna so su tabbatar da cewa sun yi tanadin haihuwar nan gaba. Wanda bawai hakan yana nufin basa basaso su sake haihuwa bane anan gaba.

Haka kuma, wasu na yanke shawarar yin hakan ne wato daskarar da kwayayen idan mace tana da wata cuta da ke shafar lafiyarta ta ɗaukar ciki.

Wannan na iya nufin cutar Sikila ko cutar Lupus da dai sauransu ko kuma idan mace na fama da cutar daji wato Cancer kuma ana yi mata gashin chemotherapy.

Akwai matsaloli dakan iya faruwa wajen daskarar da kwaikwayen halittar?

Likitoci sun ce akwai bukatar mata da susan wasu abubuwa kafin su ɗauki matakin daskarar da ƙwayayensu kamar haka:

1. Ba lallai ne ƙwayayen su sake haifar da ɗa ba anan gaba dayan da an daskarar dasu. Wato ana iya daskarar da su kuma idan aka fito da su daga ma’adanarsu domin suci gaba da aiki yanda ya kamata, se su gaza ƙyanƙyashewa.

2. Babu tsayayyun shekaru da aka ware don adana ƙwayayen amma an fi so mace ta yi lokacin tana tsakan kanin shekaru 20 zuwa 30. Sai dai likitoci sun ce kuma sun tabbatar da wannan ba wai yana nufin idan ta haura waɗannan shekarun ba za ta iya yi ba. Sedaii kawaii akwai probability na iya samun matsala bayan haura wadannan shekarun.

3. Akwai wasu matsalolin dakan iya tasowa wajen fitar da ƙwayayen. Saboda magungunan da ake amfani dasu domin inganta lafiyar ƙwayayen, mace na iya fuskantar ciwon mara kuma fitar da ƙwayayen na dan zafi ƙalilan. Haka kuma magungunan kan sa mace ta shiga halin yau farin ciki gobe takaici. Sai dai duka waɗannan matsalolin ba sa daɗewa, na wucin gadi ne.

4. Matakan da ake bi yayin daskarar da ƙwan na da tsada sosaii. Haka kuma kuɗin adana ƙwayayen bayan an cirosu daga cikin mahaifar ta mace suma na da matuƙar tsada. Don haka masu son adana ƙwan su tabbatar da suna da isassun kudade a hannunsu domin kuɗin biyan adana sun da kuma na cirewar.

THANK YOU FOR VISITING OUR SITE.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button