Politics

A yau shahararren mawaqinnan da kuka sani da Rarara ya fadi dalilin dayasa yake yiwa buhari waqa.

Fitaccen mawakinnan na siyasa a Najeriya wanda kukafi sani da Dauda Adamu Kahutu Rarara yau ya fito ya fadi gaskiyar dalilin dayasa yake yiwa general Muhammadu Buhari shugaban qasar Nigeria waqa ya ce shidai abinda yasa yake yiwa baba buhari waqa yace:

gaskiyar baba Buhari ce ta janyo hankalinsa wanda ta saka ya sa har yake yi wa shugaban na Najeriya waka (Muhammad buhari).

Dauda Kahutu Rarara ya bayyanawa duniya haka ne cikin wata tattaunawa da ya yi ta musamman da jami’an wasu gidan jarida, inda yake cewa tun yana yaro qarami ake nusantar da shi kan gaskiya da irin riqon amanar Baba Buhari kuma har yanzu da ya taso ya gani da idonsa.

Fitaccen mawakin wato Dauda Rarara ya kara da cewa burin da Baba Buhari yake da shi na gyara Najeriya da ayyukan da yake yi a yanzu ba za su kirgu ba saboda sunanan barkatai sedai idan mutum yaqi allah ya danne gaskiya.

Ko da yake a yanzu haka mawaqin ya qara da cewa yana dab da sakin wasu sababbin wakokinsa da za su bayyanawa al’ummar Najeriya irin ayyukan da Shugaba Muhammad Buhari yake yi da kuma wadanda ya kammala, wanda a cewarsa yace:

“mutane za su gamsu da ceton Najeriya da Buhari ke yunkurin yi.”

Shahararren mawaqin Rarara wanda a kwanakin baya ya karɓi kuɗin wasu ƴan Najeriya domin ya rerawan shugaban Qasar ta Najeriya Baba Buhari wata waƙa, kuma har yanzu bai saki waƙar ba duk da ya anshewa mutane kudin nasu, ya ce:

Idan da ace ƴan Qasar ta Najeriya za su karɓi ra’ayinsa da suma sun yarda dasu bari gwanin nasa ya zarce ya ƙara shekara biyar kan mulki bayan tasa wato EXTRA LEVEL domin ya kammala sauran dukkanin wasu ayyukan da ya riga ya fara.”

Mawaƙin siyasar ya qara da cewa nan gaba kadan bada daɗewa ba zai saki wasu sababbin waƙoƙin guda uku kan bayyanawa al’ummar Najeriya irin ayyukan da gwanin nasa Baba Buhari yakeyi a cikin qasar.

Sai dai bai bayyana lokacin da zai saki sababbin waƙoƙin ba, ciki har da wadda yakewa laqabi da mai taken “Shidan Buhari ta fi sha shidan gangan”

Duk da shugaban Najeriya Baba Buhari yana dab da kammala wa’adin mulkinsa amman mawaqin Dauda Kahuta Rarara ya ce bai san lokacin da zai daina yi wa shugaban waƙa ba saboda shidaii a ra’ayiinsa be taba haduwa da shugaban da yake daidai da irin nasan ra’ayin ba sama da Baba Buharin Najeriya.

Rarara ya ce ya yi wa Baba Buhari waƙoqi kimanin guda sittin da takwas 68, kuma a cewarsa bai san yawan adadin wakokin da ya yi ba a rayuwarsa baki daya dana siyasa da wadanda ba bana siyasa ba

Amma yanzu mun fara hada kan wakokin da na yi a duniya baki dayansu kaffin ji shi mawaqin.

Ban taba tsayawa na rubuta wakar Baba Buhari ba”

A cewar mawaqin Rarara: “Yawancin wakokin da nake rerawa Baba Buhari suna zuwa ne daidai da lokacin dayaxo rera waqoqin, ba wai zama nake na rubuta waka akan shi ba.

Misali ai na yi waka me taken MASU GUDU SU GUDU’ na yi tane daidaii da lokacin da Baba Buhari ya ci mulki a Najeriya a lokacin ana maganar idan PDP ta ci mulki sai dai mu gudu mu bar Najeriya to shine inayin waqar seta hau daidaii da tsarin mulkin Baba Buhari.

To bayan da Baba Buhari ya ci mulki a Najeriya muma sai muka mayarwa da sauran parties din da marta ni, a wakar, muka ce in kasan ka yi sata ka gudu wanda hakan yayi daidaii da irin mulkin da PDP tayi a baya.

Rarara ya ce a haka aka yi wakar GA BUHARI YA DAWO’ lokacin Shugaban kasa ya yi rashin lafiyane wanda ya je Qasar Landan cikin ikon allah sai aka yi sa’a ya ji sauki zai dawo, to a wannan lokacin cikin dare daya aka yi waƙar da aka ce washegari zai dawo, gaskiya ba na rubuta wakokin Buhari.”

DALILIN KARƁAR KUDIN ‘YAN NAJERIYA DOMIN YIWA BABA BUHARI WAQA.

Shahararren mawaqin me suna Dauda Adamu Kahutu Rarara fashewa ya yi da dariya lokacin da ‘yan jarida sukayi masa wannan tambaya, inda ya ce mun yi kokarin tabbatar wa da wasu mutanen masucewa farin jinin Buhari ya dusashe.

Talakawa sun amsa kira domin kuwa sun tara kudade masu yawa a wannan lokacin na mulkin Baba Buhari, in ji fitaccen mawakin, amma bai fadi nawa aka tara masa ba a asusun nasa.

“Ya ce wakar da ya karbi kudin masoya Buhari ƴan Najeriya tana nan fitowa ba da dadewa ba cikin sababbin wakokinsa da ya yi kan ayyukan da Baba Buhari yayi kuma yake kanyi.”

Rarara ya ce ya taba kin karbar zunzurutin kudi kimanin Naira miliyan 500 don ya daina yi wa Baba Buhari waka a hannun wadanda basa goyan bayan shugabancin na Buhari.

“An taba ba ni maqudan kudi kimanin naira miliyan 500 duk domin na daina rerawa Baba Buhari waka amma na ki karba, saboda duk abin da nake yi ina yi ne tsakanina da allah domin kasata kuma domin gaskiyar da Mulkin na shugaba Buhari yake dashi”.

Ya ce an sha ba shi kudi domin ya hakura da tafiyar Buhari amma a cewarsa hakan bai taba sa shi jin wani abu a ransa bama nada ya dena rerawa Buhari waqar sedaii qara masa himma da hakan yakeyi.

“‘Babban burina na ga ƙasata ta gyaru kamar yadda sauran kasashen duniya na turawa da Larabawa suke“‘ inji Rarara.

THANK YOU FOR READING THIS ARTICLE.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button