Make Money Online

CBN ta qaddamar da sabon tsarin kudin intanet na qasa (e-NAIRA) da abubuwan daya kamata ku sani akai.

Wasu daga cikin amfanin kudin na intanet su ne inganta tsarin kasuwanci, wadatuwar kudade cikin sauki da kuma saukin kasafin kudi da kuma haraji

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ƙaddamar da tsarin kuɗin intanet na ƙasar wato e-Naira ko kuma a sauwaqe nairar da ake kashewa ta intanet.

Shugaban qasar ya ƙaddamar da tsarin kuɗin intanet ɗin ne a yau ranar Litinin a Jihar Abuja, babban birnin ƙasar ta Najeriya.

Tun farko an tsara ƙaddamar da kuɗin intanet ɗin ne a farkon wannan wata, amma sai Babban Bankin na Nijeriya wato CBN ya ɗage batun zuwa gaba.

Babban Bankin CBN na Najeriya ya ce ya shafe shekaru da dama yana bincike a kan wannan tsarin na e-Naira kuma an ɓullo da tsarin ne da zummar sauƙaƙawa kowanne ɓangare na al’umma domin su gudanar da harkokin kasuwancin su“.

Tun da farko Babban Bankin Najeriya, CBN, ya ce a watan Oktoba insha allahu yan kasar za su soma amfani da kuɗin intanet dinne na e-Naira.

Babban Bankin Qasa (CBN) ya bayyana haka bayan ya haramta amfani da kudin Cryptocurrency saboda rashin gamsuwa da yadda tsarinsa yake sakamakon irin yanda bankin yaga yanda ‘yan kasar suke asara akai.

e-Naira shidai kudi ne da zai bai wa mutane damar yin harkokin kasuwanci ta intanet kai tsaye.

Tsarin zai yi aiki ne da shararren kamfanin fasaha na Bitt Inc. A kokarin shirin fara amfani da sabon tsarin kudin intanet din na e-Naira.

CBN ya zabi Bitt Inc ne daga cikin manyan kamfanonin fasaha da dama da suka fafata kuma suke kan fafatawar wajen ganin sun samu kwangilar aiki tare da babban Bankin domin samar da wannan kudi cikin tsaro da tsari mai inganci.

Sanarwar da babban Bankin Najeriya CBN ya fitar ta kuma bayyana wasu daga cikin amfanunuwan kudin na intanet din wato e-Naira da suka hada domin inganta tsarin kasuwanci a qasar. Wadatuwar kuɗaɗe cikin sauqi da kuma sauqin kasafi da kuma haraji.

Ga wasu abubuwa da suka kamata ku sani game da kuɗin intanet na e-Naira:

Kuɗin na e-Naira zai saukaka kasuwanci cikin sauki amma yana da bambanci da sauran kuɗaɗen intanet irinsu Bitcoin, baby dodge, shiba inu da dai sauransu saboda CBN ne kaɗai yake da alhakin samar da shi.

CBN ya ce kuɗin na e-Naira zai taimakawa al’ummar qasar wajen gudanar da harkokin kasuwanci cikin sauki sannnan kuma zai qunshi kowa da kowa sannan again zai bunkasa harkoki da dama kamar tsarin kasuwanci ba tare da amfani da tsabar kuɗi ba.

Haka zalika tsarin kudin intanet din na e-Naira ba ya bukatar tsabar kuɗi gaba dayansa kwata-kwata.

Haka kuma wannan sabon tsarin kudin intanet din da babban bankin qasa wato Najeriya ya gabatar na e-Naira ba ya hawa da sauka kamar saura kuɗin intanet irin su Bitcoin da sauransu, sai dai za a rika amfani da shi ne kamar yadda ake aiki da Naira a qasar.

Tun da sabon tsarin na e-Naira zai kasance irin na Naira ne, darajarsu za ta zama iri daya da ta Naira.

Haka zalika wannan sabon Tsarin na e-Naira zai kasance dabanne ba kamar yadda kuka sani ba da yadda ake bude sauran asusunan bankuna; za a samar da wata jaka da za’a rika adana kuɗin kowanne mutum daban ta hanyar ba shi wasu lambobi da shi kaɗai ne yake da irin su kamar ID kenan.

Wannan shidai Kuɗi ne da aka amincewa da kowa ya yi amfani da su a Najeriya, kuma ba zai dinga tara kuɗin ruwa ba.

Sannan za kuma a samar masa da wasu irin lambobi na tsaro da za su hana gurbata shi da yardar allah.

MUNGODE DA KASANCEWA DA HAUSATALENT.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button