News

‘Yan shi’a na shirin tayar da qayar baya a Dorayi Babba

‘Yan shi’a suna ta yunkurin suga sun tayar da hargitsi a unguwar Dorayi Babba dake a birnin Kano.

Ya kamata mutane kusan halin da ake ciki, kuma ku sanar da wasu domin daukar kyakykyawan mataki akai. Ga duk wanda ya san yadda al’amura suke wakana, zai iya bada labari akan yadda ayyukan masu bin addinin Shi’ah suke zama barazana ga tsaro da zaman lafiyar al’umma. Abinda yake faruwa kenan a Unguwar Dorayi Babba dake ƙaramar hukumar Gwale, a birnin Kano, inda waɗansu gangamin ƴan Shi’a suka bayyana a Unguwar, kuma tun a yanzu har sun fara zama barazana ga zaman lafiyar al’ummar dake zaune a yankin unguwar.

Akwai al’amura da yawa da suka faru ko kuma ace suke faruwa, wanda ya zama wajibi al’umma su sani, wadannan abubuwa sune kamar haka:-

1. ‘Yan shi’a na wancan yankin da muka ambata a sama, suna gina wata HUSAINIYYAH irin wacce suka gida a Zaria to yanzu ma haka suna gina irinta a unguwar ta Dorayi Babba, kuma suna gabatar da waɗansu tarurruka da ba’a san ko na menene ba, duk da cewa Gwamnatin Jihar Kano ta yi doka kan ta haramta dukkan ayyukan kungiyar ta Shi’a tun a ranar 11-10-2016 amma wannan kungiyar tayi mursisi ta watsar da wannan dokar.

2. Kungiyoyi masu zaman kansu, da ilahirin al’ummar wannan yanki, sun dauki matakan da suka kamata kuma wadanda basu ci karo da tsarin zaman lafiya ba, domin warware wannan matsalar, abin dai har ya kai ga zama da su ƴan shi’an domin tattaunawa da samun daidaito a tsakani, amma ƴan shi’an da sukaxo yankin sun karya duk ƙa’idojin sulhu da akayi da su.

3. Saboda sanin yakamata, al’ummar Unguwar Dorayi Babba sun kai korafe-ƙorafe wajen hukumomin dake da ruwa da tsaki wadanda zasu iya fada aji kuma wasu daga cikin hukumomin sun yi abinda ya kamata, har ma Shugabancin ƙaramar hukumar Gwale ya dakatar da ƴan Shi’an daga ayyukan nasu har a gama bincike, amma duk da haka suka bijire suka cigaba.

4. Abin da ake tsoro ya faru, domin wata rana a irin tarurrukan nasu, sai da ƴan shi’an sukayi abinda ya jawo har suka harzuƙa zukatan al’ummar dake zaune a yankin, har ya haifar musu da yamutsi da tashin hankali tsakanin su da al’ummar unguwar.

5. A yau din nan Jami’an ƴan sanda sun ziyarci waccan HUSAINIYYAH din da suke ginawa domin gabatar da wani bincike, Kuma har sun samu wadansu mugwayen Makamai masu yawa aciki, duk dayake dai da farko ƴan shi’an sun so su hana ma’aikatan shiga domin gabatar da binciken.

6. A yau Talata, akwai wata zazzafar MUZAHARA da suka shirya yi, wadda zasu faro ta tun daga Miltara har izuwa Unguwar Dorayi Babba, kuma sun tabbatar da cewa babu wanda ya isa ya hana su gabatar da taron nasu. Kuma akwai alamu dake nuna yunkurin su na afkawa al’ummar wannan yanki indai har aka barsu sukaci gaba da rayuwa a unguwar anan muke kira ga jami’an tsaro da sauran yan uwa musulmi akan su tashi su kare ƴan uwansu.

7. Ana yin zargi mai karfi akan wadansu Jami’ai akan sun hada kai da kungiyar ƴan Shi’an suna cin zarafin Malamai da al’ummar dake yankin, suna kama duk wanda suka ga dama ba tare da yin wani bincike ba, sannan kuma suna yunkurin cin zarafin manyan malaman da suke wannan yankin.

8. Akwai barazana iri-iri, ciki har da barazanar Kisa, da wadancan mutane suke yiwa al’ummar wancan yanki, bayan kamu da dauri da mutanen unguwar suke fuskanta daga waje Jami’an tsaro akan abubuwan da babu dalili.

9. A tsarin dokokin Najeriya, kowa yana da ikon yin duk abinda ya ga dama, amma kuma an hana duk abinda zai zama suka, zagi, ko batanci ga addinin wasu. Su kuwa ƴan Shi’a kowa ya san cewa dukkan addinin su ya ta’allaƙa ne akan zagin namu addinin, da batanci ga Manzon mu S.A.W, Sahabbansa da kuma matansa. Babu wani mahaluki kuwa da zai sanya ido ya kyale irin wannan barnar da taci gaba da faruwa.

10. Kamar yadda suka fara yi a Zaria, a nan ma har sun fara samun sake, ta yadda sukan iya kulle wasu yankuna a unguwar, babu wanda ya isa ya wuce, kawai don akwai wani jagora nasu a wannan yankin.

11. Dukkan abubuwan da muka ambata muku, muna da shaidu a rubuce, kuma lokaci zai yi da zamu kawo muku su daki daki.

12. Muna bukatar addu’a a wajen sauran ƴan uwa musulmi, akan Allah ya tabbatar da diga-digan mu, ya bamu sabati har sai mun kai wannan barnar ƙasa. Ka bada gudummawar ka wajen yada wannan saƙo zuwa kowanne lungu da sako na Facebook, WhatsApp, da duk in da ya sauwaka. Allah Ya taimake mu, kuma ya bamu nasara ameen.

THANK YOU FOR VISITING OUR SITE.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button