News

Hanyoyi guda 10 da zaku fara amfani da sabon tsarin e-Naira.

Babban bankin Najeriya ya bayyana wasu hanyoyin da za a yi amfani da sabon tsarin daya fito dashi na kuɗin intanet da ake kira da e-Naira.

A ranar Litinin data gabata ne shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ƙaddamar da wannan sabon tsarin na kuɗin na intanet (e-Naira).

e-Naira sabon tsarin kuɗin Najeriya ne da za a yi hada-hada ta intanet. Wannan ne karon farko da Najeriya ta rungumi amfani da kudin na intanet kai tsaye.

A cewar babban bankin na Najeriya wato CBN yace e-Naira zai zama wata hanya mai inganci ta huldar cinikayya da kudin Naira da kasar ke amfani da ita.

Hakan na nufin a matsayin al’umma za su iya amfani da nairar ne ta intanet wurin sayen kaya a kasuwa kamar yadda suka saba yi da takardar kudin naira.

Kuma ma’aikatu da manyan hukumomin gwamnati za su iya amfani da tsarin wajen karɓar kuɗaden shiga na gwamnati da kuma biyan haraji a jahar.

Wadannan hanyoyi guda 10 daya kamata ku sani sune kamar haka:

  • 1. Za a fara sauke manhajar ta e-Naira ne a kasuwar manhajar Google wato Google Play Store ga masu amfani da wayar Android kenan.
  • 2. Za a nemi manhajar e-Naira a sauke a waya.
  • 3. Bayan an sauke an buɗe manhajar sannan za’a fara yin rijista inda aka rubuta “Signup” a matsayinka na sabo kenan.
  • 4. Sannan kuma za’a zaɓi bankin da mutum yake mu’amula da shi domin yin rejistar.
  • 5. Za a saka lambar waya da kuma bayanan sirri wato security code.
  • 6. Wurin yin rijistar za’a rubuta cikakken sunan da mutum yake amfani dashi da ranar haihuwa wacce aka haifi wanda ake yiwa rejistar din kenan da asalin jihar da aka haifi mutum da kuma lambar bankin da ake mu’amula da shi da lambobin BVN.
  • 7. Idan an kammala rijistar za a tura wa mutum saƙo a adireshin Imel dinsa da ya bayar domin tabbatarwa
  • 8. Za’a amince da tsarin e-Naira idan an danna “Activate Wallet
  • 9. Domin fara aiki da e-Naira za a saka suna da lambobin sirri wanda aka yi rijista.
  • 10. Idan ya buɗe mutum zai ga asusunsa na e-Naira.

Yadda za a saka ko kuma cire kuɗi a asusun e-Naira

Wanda ya buɗe asusun e-Naira zai iya saka kuɗi a ciki nan take daga asusun sa na banki.

Kamar yadda mutum zai buɗe asusun e-Naira haka ma bankuna suna da tsari da CBN ya yi tanadi domin su.

Za a iya samun tsarinne na e-Naira a manhajar bankin da mutum yake mu’amula da shi – akwai tsarin saka kuɗi da kuma cire wa da za a zaba daga manhajar banki domin turawa da kuma cire kuɗi daga asusun e-Naira.

Mutum zai saka adireshin sa na Imel wanda aka yi masa rijista da lambobinsa na BVN sannan kuma sai a saka lambobin sirri wato security code na asusun e-Naira.

Za a turo wa mutum wasu lambobi a wayarsa da zai yi amfani da su domin tabbatar da cire wa ko saka kuɗi.

Wannan ssune matakan da akebi wajen yin rijistar.

THANK YOU FOR VISITING OUR SITE.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button