News

Bayani dalla-dalla kan yadda juyin mulkin da akayiwa shugaban qasar sudan ya faru.

Masu zanga-zangar da ke goyon bayan gwamnatin farar hula a kasar Sudan sun bazama kan tituna akan babban birnin kasar

Juyin mulkin da ya faru a Sudan, inda yanzu haka firaminista da ministocin kasar ke garƙame bayan rusa gwamnati, ya kasance rikici na baya-bayannan da ake gani ko ke girgiza kasar.

Baya ga tashin hankalin da rikicin siyasar dake faruwa a kasar, tattalin arzikin Sudan ya faɗa cikin ruɗani kan yadda abubuwa ke faruwa a kasar, ana fuskantar hauhawar farashi da karancin abinci da kuma man fetur da magunguna sakamakon juyin mulkin dake faruwa a qasar.

Juyin mulkin ya ɗaga hankulan manyan ƙasashen duniya baki daya wanda a kwanakin baya-bayan nan da suka gabata suka soma dawo da alaƙarsu da Sudan bayan tsawon shekaru na ƙaurace mata.

Ga abubuwan da ya kamata ku sani kan juyin mulkin da ya gabata a kasar.

Shin wai menene ya jawo juyin-mulkin a qasar?

Shugabannin sojoji da kuma shugaban farar-hula kadai keda ikon fada aji a kasar tun Agustan 2019 bayan hamɓarar da gwamnatin shugaba mafi daɗewa a kasar kan karagar mulkin ƙasar, wanda aka sani da Omar al-Bashir.

Sojoji sun yi tarwatsi da gwamnatin ta Omar al-basheer, sai dai zanga-zangar jama’ar ‘yan gari kan buƙatarsu ta mulki data koma hannun farar-hula sun tilastawa sojoji yin maslaha da zummar mayar da mulkin kasar kan turbar dimokuraɗiyya.

Yanzu kamata ya yi a ce ƙasar na ƙarƙashin gwamnatin riƙon-kwarya ne, inda farar-hula da sojoji za su jagoranci ƙasar tare cikin kwanciyar hankali ƙarkashin kwaminitin haɗin-gwiwar da aka kafa a kasar ta Sudan.

Amma sai ya kasance da ɓangarorin guda biyu sun fuskanci rashin jituwa a tsakaninsu amma daii har yanzu ananan ana kokarin sulhunta tsakanin jagorancin sojojin da kuma farar-hula.

Shin ma wai menene ya haddasa wannan tashin hankalin a kasar?

Shugabannin sojoji a gwamnatin riƙon-kwaryar sun buƙaci da ayi sauye-sauye daga abokan huldarsu farar-hula da neman sauya kundin tsarin majalisar tarayya ta kasar Sudan. Sai dai shuwagabannin mulkin farar-hular da ke kan rigimar mulkin a kasar sun yi watsi da wannan bukatar da sojojin sukazo da ita.

Tun a shekarar dubu biyu da sha tara 2019 sojojin suketa kokarin aga anyi tarwatsi da kundin tsarin mulkin gwamnatin farar-hular wanda ba’ayi nasarar yin hakan ba, na baya-bayan nan daya gabata shi ne wanda aka gani a watan da ya gabata.

Babban jagoran mulkin farar-hula na kasar Sudan, Firaminista Abdallah Hamdok, ya zargi masu biyayya ga shugaban mulkin farar-hular Omar el-Bashir, wanda akasarin su ake cewa suna cikin sojoji, hukumomin tsaro da cibiyoyin gwamnatin kasar wanda daman kowa yasan da ba’a iya juyin mulki se idan harda sa hannun mabiya bayan gwamnatin da takecin.

A makonnin baya-bayan nan da suka gabata an fuskanci zanga-zanga daga masu goyon bayan sojoji a babbab birnin kasar Khartoum, da kuma wasu dandazon jama’a da suka fito domin nuna na su goyon-bayan ga firaministan kasar.

Masu zanga-zangar goyon-bayan sojoji sun zargi gwamnati da nuna gazawa wajen sake farfaɗo da da kundin tsarin mulkin ƙasar.

Kokarin Mista Hamdok na sake farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar ciki har da zaftare wasu tallafin man fetur (SUBSIDY) bai samu gamsuwar mutane ba.

Rikicin siyasar Sudan abu ne da ya jima yana kassara qualitin ƙasar.

A shekarun baya da suka gabata ba masu nisa ba sosai rabuwar kawuna tsakanin jam’iyyun siyasa da gazawa wajen haɗa-kai sun buɗe kofa da bai wa sojojin kasar damar shiga harkar siyasar ƙasar, da aiwatar da juyin-mulki da sunan kokarin dawo da ƙasar kan turba madaidaiciya a cewar mai shari’a Magdi Abdelhadi.

A yau Sudan, akwai akalla jam’iyyun siyasa daidai har guda tamanin cif 80.

Irin wannan rabuwar kawuna da ɓangarancin da suke faruwa sune suka taka rawa a gwamnatin riƙon-ƙwarya, abin da ya kai ga samun rabuwar kan tsakanin sojoji da kuma farar-hula har aka kai ga matsayin da ake ciki yanzu haka a kasar.

Menene yake faruwa a yanzu haka cikin kasar?

Jagoran sojojin da suka yi juyin mulkin a kasar ya gabatar da jawabi da ke ayyana dokar ta baci da rusa majalisar ministoci da gwamnonin kasar.

Janar Abdel Fattah Abdelrahman Burhan ya ce: za kuma a gudanar da zaɓuka a watan Yulin shekara ta dubu biyu da ashirin da uku 2023.

Rahotanni da dama na cewa an garƙame firaminista Hamdok bayan hamɓarar da shi, da wasu ministocinsa masu yawa. Sannan sojojin sun karɓe duk wata ragamar tashoshin gidan talabijin da kuna rediyo na ƙasar Sudan din. An kuma katse layukan intanet baki daya.

Ƙungiyar haɗin-kan Afirka, AU da kuma Majalisar Dinkin Duniya UN da Tarayyar Turai da kuma Ƙungiyar ƙasashen labarawa UAE da Amurka US sun yi alla-wadai da juyin-mulkin daya gabata na kasar Sudan.

Shine menene zai iya faruwa nan gaba sakamakon wannan juyin mulkin daya afku a kasar ta Sudan?

Juyin mulkin daya gabata ba lallai ya kasance karshen rikicin ƙasar da take fama dashi ba, a cewar mai sharhi kan ƙasashen Afirka Alex de Waal, yace:

kalmomin da ke kasancewa kamar ƙarfafa gwiwa ga farar-hula sune, A duk lokacin da sojoji suka yi irin wannan yunkuri mutanen kasar na fantsama ne kan tittuna da ƙoƙarin daƙile su domin hana wucewa kuma ina da yaƙinin cewa tarihi na iya sake maimaita kansa a wannan karon. ya shaidawa wasu gidan jaridu hakan.

A cewar wasu bayanai da ma’aikatar labarai ta wallafa a shafinta na Facebook, firaministan kasar wato Hamdok ya yi kira ga ‘yan ƙasar dasu fito su marawa gwamnatinsa baya.

Hotuna da rahotanni da ke fitowa daga babban birnin qasar Khartoum na nunawa duniya yadda masu zanga-zangar suka fantsama tsulum akan manyan titunan babban birnin qasar Sudan din.

Kuma an tura sojoji kowanne yanki domin taƙaita zirga-zirga a fadin kasar.

A watan Yunin shekarar dubu biyu da sha tara 2019, kafin cimma daidaito da kafa gwamnatin riƙon-ƙwarya, sojojin sun buɗe wuta kan masu zanga-zanga a Khartoum da kuma kashe kimanin mutum saba’in da bakwai 87.

Jimamin wannan rana wani abu ne da wadanda abin ya faru kan idansu kuma ya shafi sauran ‘yan uwansu ba zasu taɓa mantawa dashi ba a fadin rayuwarsu har abada.

Duk da dai cewa duniya rankatakaf sunyi allah wadai da irin wannan juyin mulkin daya faru a kasar kamar irin su majalisar dinkin duniya da yankin nahiyar Africa da kuma daular Larabawa suma duk sunyi allah wai da wannan mummunan abinda ya faru a kasar Sudan.

Allah ya tsare ya kuma kiyaye gaba ya kiyayemu da mugun ji da mugun gani ameen.

THANK YOU FOR VISITING OUR SITE HAUSATALENT.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button