News

Yanda ‘yan ta’adda suka tarwatsa wasu garuruwa sama da guda 10 a jihar Zamfara.

A hare-haren da ‘yan fashin daji suke kaiwa gari gari sun tarwatsa al’ummar wasu garuruwa sama da goma (10) na yankin karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara, bayan karkashe wasu mutane da sace dabbobin mutane da sukayi tare da qona shaguna da sukayi da dai sauransu da ‘yan fashin dajin suka yi.

Yanzu haka yanayin da ake ciki dai jama’ar garuruwan da abin ya shafa na jihar Zamfara suna can suna zaman gudun hijira a wasu ƙananan hukumomi da ke makwaftaka da karamar hukumar ta Zurmi fake jihar Zamfara.

Bayanan da aka tattara sun ce yanzu haka halin da ake ciki jama’ar garin Ƴan Ɓuki da kuma sauran yankunan karamar hukumar da dama sun shiga halin ha’ula’i sun shiga hali marajin dadi tun bayan lokacin da ‘yan bindigar suka dake kan tsaurara hare-haren da suka kai musu a ranar Lahadin da ta gabata ta wannan satin.

Wani bawan allah mazaunin garin ƴan Ɓuki da ya buƙaci mu sakaye sunansa ba semun fadawa duniya ko wane ba ya shaida mana cewa garuruwan da lamarin ya shafa sun haɗar da

 • 1. Ƴan Ɓuki.
 • 2. Ditsi.
 • 3. Kada Musa.
 • 4. Gidan zago.
 • 5. Marmaro.
 • 6. Dada.
 • 7. Maduba.
 • 8. Kwata.
 • 9. Oho.
 • 10. Fushin Buku.
 • 11. Gandasau.

Dukkan wadannan garuruwa dana lissafo ina mai tabbatar muku da cewa yanzu babu kowa da yake rayuwa a cikinsu, a halin da muke ciki yanxu haka sun yi gudun hijira, yanzu idan ka je garin Ƙauran Namoda za ka tabbatar da su ne suka taru a can sukaje suka tattare, sannan wasu suna Gusau babban birnin jihar ta Zamfara.

Mai bayar da shaidar ya kara da cewa:

A halin da ake ciki duk wadanda ‘yan bindigar suka gani ko suka kama a waɗannan garuruwa suna kashe su ne ko kuma su kama su sannan kuma su tafi da su daji, suna zazzagayawa, har suna barazanar cewa duk wanda ya je shiga gona don dibar gyada ko dawarsa, to ya sani za su kashe shi

A cewarsa:

Yanzu haka akwai mutane kimanin 45 wadanda suka dauki mutanen garin Dutsi, wadanda suke can a hannunsu, babu kuma wani mataki da matakan tsaron da aka dauka har zuwa wannan lokaci suka bayar kan wannan lamari.

Shi ma wani mutum da yake zaune a garin na Yan Ɓuki da ya tsallake rijiya da baya ya shaida mana da cewa sun shiga garin ne da yawa a kan babura suna buɗe wuta kan mai uwa da wabi babu ruwansu da irin adadin mutanen da zasu kashe ko kuma su jikkata da irin wannan mugun harin da suka kai.

Suna bin mutane har gida-gida suna fasa dakunan su suna shiga, kuma da sun yi arba da mutum ba abin da suke yi illa su harbe mutum ya mutu su yi gaba, su je su kwashi dabbobi da dukkanin abubuwan da sukasan na amfani ne daganan kuma se su qara gaba, sun tafi da awaki sun kai kimanin sama da ɗari biyar 500, saniya kawai, domin tumakai kuwa sun kwashi sama da guda dubu wadda suka tafi da su“. inji wannan bawan allah me shaidawa masu gidan jarida.

Sannan ya kuna qara da cewa washe garin ranar da suka kai harin sai da muka binne mutane bakwai da suka gamu da ajalinsu yayin wannan farmaki da ‘yan bindigar dajin suka kai.

To sai dai a tattaunawarsa da wannan gidan jaridar namu, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ya ce sun samu labarin abin da yake faruwa a yankin na Zurmi, har ma an aika da jami’an ‘yan sanda kusan mota bakwai 7 domin tunkarar ‘yan bindigar duk da dai Jami’an namu basu sami wadannan mugwaye mutanen ba.

Sun je sun yi rangadi nadan wani lokaci domin tabbatarwa da dukkanin abubuwan da suke faruwa da kuma qarawa mutane kwarin gwiwar cewa jami’an tsaro na sane da duk abubuwan da suke ta faruwa a wannan yankin, kuma a shirye suke da bada kaiya ga rayukansu da dukiyoyin su, inji kakakkin ‘yan sandan.

Allah shi kyauta sannan kuma yayi mana jagora baki daya.

THANK YOU FOR VISITING OUR SITE HAUSATALENT.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button