Politics

Buhari yace ya rantse da Al-Qurani bazeyi tazarce ba.

Shugaban Qasar Najeriya Muhammadu Buhari ya yi rantsuwa da girman Al-Qurani da furicin cewa ba zai zarce a mulkin Najeriya karo na uku ba tunda dai ‘yan kasar basa buqatar hakan daga gareshi.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kan harkokin yaɗa labarai wato wanda kukafi sani da Garba Shehu, ya fitar ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce Shugaban Najeriya Baba Buhari ya bayyana hakan ne a yayin gabatar da wani taro da ya yi shi a babban gari me tsarki cikin saudiyya Makkah da shi da wasu zaɓaɓɓun ‘ƴan Najeriya mazauna garin.

Shugaban yace:

Ni Gen Muhammad Buhari Na ranste da girman da allah yayiwa Al-Kur’ani mai tsarki zan yi aiki da abin da kundin tsarin mulkin kasata ya tanada kuma zan tafi nabar mulkin kasar a daidai lokacin da wa’adina ya ƙare

Saboda hakama ba na so wani daga cikin magoya bayana ya fara yin magana game da wannan al’amarin ko kuma yinqurin gudanar da kamfen a kan tsawaita abin da ba ya cikin kundin tsarin mulkin Najeriya. Ba zan lamunta da haka ba.

Haka zalika, Shugaba Buhari ya bayyana irin goyon bayansa ga ƙoƙarin inganta amfani da fasaha wajen gabatar da zaɓukan ƙasar a zaben da za’a gudanar me zuwa.

“Samar da na’ura me gudanar da aikinta da kanta kan tantance masu kaɗa ƙuri’a da rijistar masu yin zaɓe ta intanet addu’o’ina ne da Allah Ya amsa na cutarsa da aka yi sau uku a wasu zaɓuka a baya,” a cewar shugaban kasar a wata sanarwa.

Hakanan shugaban ƙasar ya ƙara da cewa:

Bayan faɗuwar da na yi a karo na uku bayan gudanar da zabukan kasar, sai na ce,Allah Yana nan kuma yana ganin abinda yake faruwa shine majority bancin lamurana Abokan hamayyata sun yi min dariya bayan zaben amma Allah Ya amsa addu’o’ina ta hanyar qirqiro da wata fasaha. A wannan gaɓar, babu wanda zai iya sace ƙuri’a ko sayanta da yardar allah

Shugaba Muhammadu Buhari ya kammala ziyarar tasa ne a qasar Saudiyya da kuma yin Sallar Juma’a a Masallacin Ka’aba, inda ya ce zai ci gaba da bin kundin tsarin mulki sau da ƙafa insha allah a duk ayyukansa kuma zai dinga sa ido da bibiyar ayyukan ministocinsa kamar haka.

Sannan kuma ya bayar da tabbaci a wajen taron cewa zai yi duk mai yiwuwa wajen bayar da inganci kan rayuwar ‘yan Najeriya a cikin sauran lokacin da ya rage masa na wata goma sha takwas 18, “zan yi hakan ne saboda ƙasar da kuma al’ummar da suke cikinta.

Shugaban ƙasar ya kuma yaba wa ‘yan kasar tasa Najeriya mazauna Saudiyya kan wakiltar ƙasar yadda ya kamata wajen gyarawa da kankaro ƙimarta a idon duniya baki daya.

Shugaban yace da a dinga yi masa adalci kan al’amuransa

Sannan kuma ya yi magana kan masu sukarsa a kasar tasa Najeriya inda ya ce su dinga yi wa mulkinsa adalci a koyaushe, yana mai cewa su duba yanayin tsaro a yankunan arewa maso gabas da kudu maso kudu a shekarar 2015 da kuma yanzu yanayin da ake ciki da yadda abubuwa suka inganta cikin kasar da samar da zaman lafiya.

“Babbar matsalata a kasar ita ce arewa maso yamma, yayin da mutane ke kashe junansu da yi wa juna sace-sace ba tare da wani dalili ba kuma babu abinda suka rasa

“Dolene na yi musu da tsauri-tsauri kuma zan ci gaba da zama mai tsauri har sai mun dawo da su kan hanya, mun daidaita musu sahu,” inji shugaban kasar.

A ƙarshe Shugaba Muhammad Buhari ya nemi da ƴan Najeriya mazauna yankin Saudiyya da suci gaba da girmama doka su zama masu bin tsari, kuma “kar su yi duk abin da zai jawo ɓaraka da dangantakar da take tsakanin ƙasashen guda 2 biyu da aka shafe shekaru masu yawa ana ɗasawa kan tafarkin daidaito”.

Shugaban ƴan Najeriya mazauna kasar ta Saudiyya, Dr. Abdulkadir Maikudi, ya nemi da shugaban da ya taimaka wajen samar da kayayyakin aiki musamman na kimiyya da fasaha a makarantun boko na ƴan Najeriya mai zaman kanta a ƙasar.

Jakadan Najeriya na Saudiyya Ambassador Yahaya Lawal da wani babban jami’in ofishin jakadancin na Jiddah, Ambassador Abdulkarim Mansur, sun bayar da shaida kan kyawun halin kusan mutum miliyan 1.5 ƴan Najeriya da ke can zaune a kasar ta Saudiyya.

“Ƴan Najeriya ƙwararru suna gudanar da abin kirki kuma suna halayya ta gari da ke qara kankaro ƙimar ƙasar tasu Najeriya.”

Thank you for visiting our website hausatalent.com.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button