Technological Ideas

Duniya ta farko da aka gano a cikin Milky-way bayan lissafin wadanda ake dasu.

Doctor Rosanne Di Stefano dashi da sauran abokanan aikinta likitoci sun nemi su gano yadda hoton da aka dauko na wasu abubuwa a binciken da aka gabatar suka dusashe.

Malamai masana ilimin sararin samaniya sun gano wata alama wadda take nuni da gano wata duniyar bayan dandazo da tarin taurarin da duniyarmu da muke zaune a ciki wato a wajen na Milky-way.

Akalla an gano kusan taurari kimanin guda dubu biyar 5,000 a saman taurarinmu da muke dasu, amma dukkaninsu suna kusa da hasken dandazo da tarin hasken taurarin da muke ciki ne.

Duniyar da aka gano yanzu haka alamarta, tana da matukar girma itama kamar girman duniyar Saturn. An gano ta ne ta hanyar amfani da na’urar hangen nesar Chandra X-Ray, kuma tana cikin manya-manyan dandazon taurari na hamsin da daya 51 ne cikin jerin taurarin.

Kuma tana da nisan kimanin gudun tafiyar haske na shekara miliyan ashirin da takwas 28 daga hasken taurarinmu da muke dasu.

Wannan sabon binciken da aka gabatar kwanannan ya ta’allaka ne da yanayin tafiya, inda wucewar sabuwar duniyar ta gaban wani tauraro ya tare hasken wasu taurari saboda girmanta. wanda hakan ya haifar da dusashewar hasken taurarin.

Wannan ne ya taimaka wa na’urar hangen nesan da akayi amfani da ita wajen dakko hoton.

An kuma yi amfani da wannan salon ne wajen gano dubban wasu duniyoyin daban.

Doctor Rosanne Di Stefano da sauran abokan aikinta sun nemi gano yadda hoton da aka dauko na wasu abubuwa suka dusashe.

A cikin wannan hasken da aka dakko na wannan layin, akwai wani karamin tauraro ko kuma muce muke baƙin rami da ake jan iskar gas daga taurarin da suke zagaye a kusa da shi.

Wani abu kuma da ke kusa da dan karamin tauraron ko baƙin ramin sai ya dauki zafi sosai, sannan ya ƙara haske ta dalilin sanadiyar hasken daukar hoto.

Saboda wajen da yake bayar da hasken daukar hoton ƙarami ne sosai, duk wata duniya da za ta wuce ta gabansa, za ta iya tarewa ne da yawa daga cikin hasken ko kuma ta ma tare shi baki daya, wanda ya saukaka gano wucewar wani abu.

Masanan masu binciken sun yi amfani da wannan tsarin ne domin gano sabuwar duniyar da suke binciken mai suna M51-ULS-1.

Tsarin da muka bi shi kadai ne a yanzu tsarin da za a iya bi wajen gano wasu dandazon tarin taurarin,” kamar yadda Doctor Di Stefano ta babbar cibiyar Binciken Taurari na Harvard-Smithsonian da ke qasurgumiyar Jami’ar Cambridge da ke qasar Amurka ta bayyanawa gidan jaridar mu hakan.

Wannan wani tsari ne na daban, wanda kuma yake da yanayi mai kyau da za’a gano wasu duniyoyin masu makwabtaka da layukan hotunan da masu binciken suka gano duk da kasantuwar nisansu kuwa. wanda daga nan kuma za mu iya gwada yanayin haskensu domin tantancewa.

An kaddamar da wannan abin daukar hoto daga nesa (Microscope) na Chandra a 1999

Yiwuwar nemo wasu duniyoyin a nan gaba.

Wannan layin yana dauke ne da wani baƙin rami ko karamin tauraro da yake zagaya wani tauraro mai nauyi da ke kusa da shi wanda a qalla yakai kusan ninkinsa sau ashirin 20 sama da yadda rana ke yi.

Wannan karamin tauraron, babban tauraro ne ya rage girman sa ya koma haka.

Yana zagayan ne na awa uku acikin ko wacce rana, wanda a wannan lokacin ne hasken daukar hoton yake komawa farko domin ya dawo baya.

Da wannan ne da kuma sauran bayanai da aka tattara, malamai masu ilimin sararin samaniyar suka gano cewa duniyar da suke bincike a kanta din girmanta ya yi kusa da Saturn, kuma tana manne ne da karamin tauraron ko baƙin ramin da nisan sa kusan ninki biyu da nisan da Saturn din take tazarar ta daga rana.

Doctor Di Stefano ta ce wannan tsarin da ya taimaka mana wajen samun nasarar gano wasu duniyar a hasken dandazon tarin taurarin namu, yana daina aiki ne idan ana amfani da shi a wasu dandazon taurarin na sararin samaniya.

Wannan ba zai rasa nasaba ba da cewa girman nisan da ke tsakani yana rage karfin hasken da ke kaiwa ga na’urar hangen nesan.

Sannan kuma yana nufin akwai wasu abubuwa da suka taru a cikin dan ramin wajen (kamar yadda aka gano daga wannan duniyar nan da muke ciki Earth) wanda hakan ya sa ake shan wahala wajen gano wasu taurarin.

Da wadannan hotunan ne ta ce:

watakila akwai wasu alamun da dama da za’a iya gani a dandazon taurarin. Amma dai wasu daga cikin alamun suna da haske matuka da za su isa a samu mu dakko hoton hasken da ke ciki.

“A karshe, manyan hasken da ke fita daga karamin wajen, wucewar wata duniyar za ta iya kasan cewa ta dan tare shi, ko kuma ta tare dukan haskensa kamar yadda muka gani a cikin namu binciken.”

Masu binciken sun kara da cewa ana bukatar karin bayani domin tabbatar da binciken nasu.

Sai dai wani kalubale shi ne, yanayin girman layin duniyar ya saka ba za ta sake wucewa ba har sai nan da kusan shekaru a qalla guda saba’in masu zuwa 70, wanda hakan ke nufin takaita yiwuwar bibiyar binciken a nan kusa.

An wallafa wannan binciken ne a cikin Mujallar Nature Astronomy.

Wani karin bayanin kuma da malamai masanan sararin samaniyar suka gano duk dai a cikin wannan binciken daya gabata shi ne, kasancewar iskar gas da kuma ƙura da ke wucewa ta gaban wajen da aka dakko hoton ma na iya janyo dusashewar hasken da suka gani.

Amma dai sun ce suna tunanin da wahala hakan ya faru domin alamun da suka gani a yanayin aikin nasu da suka gabatar ba su yi daidai da yanayin iskar gas din ba.

Julia Berndtsson na Jami’ar Princeton da ke New Jersey, wanda ke cikin wadanda suka wallafa binciken yace:

Muna sane da cewa wannan bincike ne mai muhimmanci, don haka muke kira ga sauran manyan malamai masana sararin samaniya da su yi dubi ga bayanan cikin tsanake.

Muna tunanin muna da hujja mai karfi, kuma wannan shi ne tsarin binciken kimiyya.

Dr. Di Stefano ta ce:

sababbun na’urorin hangen nesan da muke dasu ba za su iya magance matsalar da ake fuskanta ba ta duhu da taruwar abubuwa a waje daya, don haka suke tunanin amfani da daukar hoto din ne zai cigaba da zama mafi sauki wajen gano wasu duniyar a cikin wasu tarin dandazon taurari cikin sararin samaniyar.

Sai dai kuma ta qara da cewa akwai wani tsari da ake kira da Microlensing da zai iya taimakawa wajen saukakewa masanan wajen gano sababbin wasu duniyoyin.

An wallafa wannan binciken ne a Mujallar Nature Astronomy.

MUNGODE DA ZIYARTAR WANNAN SHAFIN NAMU ME ALBARKA (HAUSATALENT).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button