Politics

Jam’iyyar PDP tace ta kammala shirinta na fara babban taronta a ranar wannan asabar din.

Shirin gabatar da babban taron jam’iyyar PDP mai hamayya a Najeriya ya kankama a Abuja capital territory babban birnin ƙasar ta Najeriya, inda ake sa ran ƴaƴan jam’iyyar daga ko ina a faɗin kasar ta Najeriya za su zaɓi manyan shuwagabannin ta.

Wannan taron yana zuwa ne bayan da wasu ‘yan jam’iyar ta PDP suka shigar da kara a kotu domin a dakatar da gudanar da taron, sai dai ana kamar i’gobe za’a gudanar da shi a gaban kotu ta yi fatali da buƙatar tasu, ta ce a ci gaba da shirin yin taron.

Sakataren babban jam’iyyar ta PDP na ƙasa Sanata Umaru Ibrahim Tsauri, ya shaida wa gidan jaridar namu da hausa cewa an kammala dukkan wani shiri abin da kawai ake jira shi ne fara tantance waɗanda ake da buqatar za su gudanar da zaɓen, kana su ƙada ƙuri’a idan an jima.

A cewarsa tasa yace:

Muna yi wa Allah subaha nahu wata’ala godiya, domin matsayin da muke ciki a yanzu ba’a kan shi muke ba a kwanakin baya, jiya kamar yanzu muna tunanin shin za a yi taron ko ba za a yi ba saboda muna qila waqala don ana ta maganar kotu za ta iya dakatarwa, amma ga shi cikin ikon Allah kotu ta ce za a iya ci gaba da yi wanda hakan ya sakamu munyi farin ciki sosaii.

Sakataren jam’iyyar gaba daya ta PDP na Najeriya ya ƙara da cewa daman babban kalubalen da suke fuskanta a kan taron shi ne yiwuwar hanawa, ”domin shari’ar kamar mace ce mai ciki, amma saidai mu ba zamu yarda mu yi ƙasa a gwiwa ba, sai da mukayi kokari muka ga ko me za ta iya haifar mana bayan mun kammala shirin suna, to yanxu Alhamdulillahi abin da muke da bukata mun samu, kuma an kammala komai cikin ikon allah za a yi wannan taron.”

Shuwagabannin jam’iyyar gaba daya mutum ashirin da daya ne 21 za’a zaɓa, da suka hada da ‘yan kwamitin gudanarwar jam’iyyar su mutum goma sha uku ne 13, da mataimakan su kuma suma guda takwas 8, wanda jimillar su shine suka kama guda ashirin da daya 21 kamar yanda muka fada a baya kuma su ne za su jagoranci jam’iyyar ta PDP daga ranar takwas 8 ga watan Disamba har zuwa zaɓen shekarar dubu biyu da ashirin da uku 2023.

SanataUmar Ibrahim Tsauri yace :

Dukkanin wasu matakai da ake iya bi na ganin taron nan ya yi nasara to tsakani da Allah an bi shi, kuma an kawo matsaya abin da kawai muke jira yanzu shi ne anjima a tantance masu jefa ƙuri’a, a kaɗa kuri’ar a kuma zaɓi shugabannin da za su jagorance mu zuwa samun nasara a zaɓukan 2023 me gabata idan Allah ya kaimu

Ya ce an dauki dukkanin wasu matakai wanda suka kamata da’a dauka kan kawo harkar tsaro da abinci da wurin zama da komai don gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

THANK YOU FOR VISITING OUR SITE HAUSATALENT.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button