Health

Jami’an lafiya na Amurka sun qara zurfafa bincike kan asalin cutar COVID-19.

Manya-manyan hukumomin tattara bayanan sirrin kasar Amurka sun bayyanawa duniya da cewa duk da yake ba lallai ne a binciken da zasu qarayi su gano yadda korona ta samo asali ba, amma sun tabbatar da cewa ba wai an ƙirƙiro cutar bane don cutar da bil adama kamar yadda ake ta raɗe-raɗi a fadin duniya baki daya.

A wani ƙarin bayani da aka samu kan asalin cutar ta covid-19, ofishin darakta janar na hukumar tattara bayanan sirrin ta Amurka ya ce kusan dukkanin hujjojin da aka tattara a halin yanzu ba hujjoji bane gamsassu da za’a dauka a dogara dasu amma dai ananan anata ci gaba da gudanar da wannan binciken.

Kamar yadda Shugaban kasar Amurka na yanzu Joe Biden ya buƙata, wannan wani bincike ne da akeyi da kuma neman ƙarin bayani wanda hukumar tattara bayanan sirrin ta yankin Amurka ta yi kan bin diddigi da salsala da asalin korona virus cutar data addabi duniya baki daya.

Masu tsawaita bincike da masana sun cimma matsaya kan wasu abubuwa biyu inda tunaninsu da fahimtarsu ta zo ɗaya kan batun cutar ta covid-19, inda a farko dukkaninsu ma’aikatan lafiyan suka taru suka yi amannar cewa ko dai cutar ta yaɗu ne daga dabba zuwa bil adama ko kuma ta sulalo ne daga daƙin gwaje-gwaje ta yaɗu kuma harta addabi duniya.

Sai dai har yanzu batun da ake ciki dukkanin su sun kasa cimma matsaya kan ko ta wace hanya ce za’a iya cewa ta fi yiwuwar zama gaskiyar zance dangane da wannan hasashen guda biyu.

Masu tattara bayanan sirri na kasar ta Amurka sun tsayu ne kan cewa ba wani mahaluƙin da ya zauna a ɗakin gwaje-gwaje ya ƙirƙiro wannan cuta kuma ba daga ƙwayoyin hallita aka samar da ita ba saboda a iya binciken da mukayi mun gano babu wani mahaluki da za’a iya cewa shine ya qirqiro wannan cutar idan kuwa da ace wanine ya shiga dakin bincike ya qirqiro ta da tuni shika yasan yanda zeyii ya kashe wannan wutar dan kansa ko kuma domin iyalansa wanda dole shima wannan cutar ta covid-19 shima ta addabeshii, koda kuma ba zayi dan lafiyar ‘yan uwansa da iyalansa sannan kuma dashi kansa to dole ze fito ya nunawa duniya cewar yasan ta hanyar da zebi ya daqilar da wannan babban annobar kodan ya samu wasu irin maqudan kudade sannan kuma haka ze saka yayii suna a duniya.

Haka kuma a iya binciken nasu da sukayi, sun ce babu wani tabbaci kan zargin da ake yi wa masu bincike a wani daƙin gwaje-gwaje da ke birnin Wuhan na China kan cewa suna da hannu dumu-dumu a wajen yaɗuwar cutar a duniya.

Amma jami’an Amurka sun ce akwai yiwuwar su koma su ci gaba da bincike domin samun ƙarin haske kan wasu abubuwan da har yanzu suke cikin duhu musamman ma idan an sake samun wasu hujjojin.

Allah ya bada ikon gano wannan binciken da akeyi saboda ta hakane kawai idan aka gano asalin cutar ta Corona-Virus sannan hakan ze bada damar samar da maganin cutar.

THANK YOU FOR VISITING OUR SITE HAUSATALENT.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button