News

Wannan shine jemagen daya lashe gasar tsuntsaye ta duniya a wannan shekarar 2021.

Jemagen daya lashe gasar tsuntsayen na wannan shekarar yanada tsawon wacce tsayin jelar bai fi girman ɗan yatsan hannu ba.

Wani mutum me kiwon tsuntsayen kuma yake koya musu tseren na gudu ya lashe kyautar tsuntsu na wannan shekarar a New Zealand, abin da ya jawo cecekuce tsakanin al’ummar kasar.

Jemagen daya lashe gasar ta bana mai tsawon jela ne kuma ya yi nasarar ne a wata ƙuri’a da aka kaɗa ta intanet.

Waɗanda suka haɗa gasar ta tseren tsuntsayen sun saka jemagen daya lashe gasar ne, a matsayin ɗaya daga cikin dabbobin ƙasa kuma haifaffun kasar ‘yan asalin ƙasar New Zealand, domin fito da shi a matsayin halittun da ke fuskantar barazanar ƙarewa a bayan ƙasa wanda hakan yasa suka shirya wannan wasan domin dago da martabar wannan halittar a duniya wato Jemagu.

Sai dai nasarar da wannan Jemagen yayi ta ɓata wa wasu mazauna kasar da kuma duniya baki daya rai, inda wasu ke cewa ƙasar ta “haukace”.

Wasu kuma masu ƙaunar dabbobi a dandalin shafin su na Twitter sun fusata, suna kiran gasar da aka gudanar da “shirme”, ko kuma “maguɗi”, da kuma dai sauran kalaman da ba za a iya bayyanawa ba.

Wasu kuma na cewa wannan ai wata sabuwar samun nasara ce ga jemagu bayan sun daɗe suna fafatawa a gasar ba tare da samun nasara ba amma wannan karon Jemagun sun lashe gasar.

Ƙungiyar Forest and Bird wadda ta shirya gasar, ta ce ba ta saka wannan jemagen daya lashe gasar a cikin gasar ba don ta ɗaga darajarsu musamman a lokacin annobar COVID-19.

Gasar da ke zaɓo gwarzon tsuntsun shekara ana shirya ta ne domin wayar da kai da kuma fitowa fili da dabbobin da ke fuskantar barazanar ƙarewa a qasar da aka gabatar da wannan gasar wato New Zealand.

Cikin wani yunƙuri na kauce wa abin da aka saba yi a kimiyya, Qungiyar ta Forest and Bird ta yanke wata shawarar saka dabbobin dan dariyar ƙasa a wannan shekarar a karon farko kuma cikin ikon allah suka lashe wannan gasa ta tsuntsayen duniya baki daya suna masu cewa su ma sun fuskanci ƙalubale suma kamar yanda sauran tsuntsaye suke fuskanta suma idan suka lashe gasar dan haka suna ganin wannan ba wani abu bane da za’a dinga cewa waii kasar ta haukace ko kuma anyi magudi.

Ana kiran jemagen ne da pekapeka-tou-roa kuma bai fi girman ɗan yatsa ba gaba dayansa. Ya dauki tsawon wata aku cirr kafin ya yi nasarar lashe wannan gasar.

Jumillar fiye da kimanin mutum dubu hamsin da shida da dari bakwai 56,700 ne suka kaɗa ƙuri’a a zaɓen yayin da jemagen ya samu fiye da quri’a dubu bakwai daidai 7,000 cikin mutanen da suka kada quri’ar, inda ita kuma akun ta samu kimanin mutum dubu hudu 4,000 da ɗoriya bayan ta lashe gasar a shekarar da ta gabata.

Ba wannan ne karon farko da gasar ta haddasa cecekuce ba a kasar dama duniya baki daya daman an saba samun irin wannan sabanin kusan duk shekarar da aka gabatar da wannan gasar.

A shekarar dubu biyu da goma sha tara 2019, an samu wasu ƙuri’u da aka kaɗa daga can kasar Rasha, abinda ake fargabar maguɗi.

Masu shirya gasar sun aminta da cewa akwai yiwuwar masoya tsuntsaye ne suka jefa ƙuri’a daga can kasar ta Rasha, maimakon masu kutse da ke neman yin maguɗi.

Da wwannan muka kawo muku qarshen abinda ya faru a wannan gagarumar gasar da aka gabatar.

MUNGODE DA ZIYARTAR WANNAN SHAFIN NAMU ME ALBARKA HAUSATALENT.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button