Relationships

Abin kunya: wasu qawayen amarya sun saka ango ya saki amaryarsa a daren farko.

Wasu shaidanun qawayen amarya sun saka angon ya saki amaryar tasa a daren farko wato daren da aka kai masa matar tasa dakinsa ba tare da bata lokaci ba.

Wani Ango ne dai ya saki Amaryar tasa saki ɗaya a daren da aka kawota tun kafin ya shiga ɗakin nasa ya ganta sakamakon wani cece-kuce daya faru tsakanin abokanan angon da kuma qawayen amarya.

Hakan dai ya biyo baya ne bayan da ƙawayen Amaryar suka kulle ƙofar dakin amaryar suka ce sam bazasu buɗe ƙofar ɗakin nan ba har sai an biyasu kuɗin al’ada da ake biya bayan ankai amarya dakinta wato kudin sayen baki har naira dubu ɗari biyu (₦200,000).

Da jin haka kuwa sai abokan Ango suka yi ta luguden laɓɓa wato cacar baki da ƙawayen Amaryar don neman ayi musu sassauci kan farashin da suka fada. Bayan da Angon yaga abin ya ƙi ci kuma ya ƙi cinyewa kuma gashi dare yana ƙara tsawo ana taci gaba da ɓata lokaci tunda ƙawayen sun kafe kan sai an biya su kudin siyan baki kimanin Naira dubu dari biyu ₦200,000 yaga dai da gaske sukeyi se an basu hakan sannan zasu bude musu kofar sai yace a basu naira dubu talatin (₦30,000) a wuce wajen kawai suyi haquri.

Bayan an ƙidayo ma’ana an qirgo kudin Naira dubu talatin aka ce gashi suyi haquri su buɗe ƙofar sai kawai ƙawayen Amaryar suka ƙeƙasa ƙasa sudai allankatafur suka ce basu yarda ba, Naira dubu talatin (₦30,000) tayi kaɗan a siyam bakin wannan kyakykyawar amaryar kuma ‘yar dangi. Don haka ba zasu buɗe ƙofar ba sai an ƙaro musu kudin.

Daga nan sai Angon ya kira Amaryar tasa a waya har sau biyu 2, ita kuma taƙi ɗaga wayar Angon nata.

Abinka da ƙaddara ta riga fata abinda allah y rubuta dole seya afku, aikuwa cikin fushi saboda kiran nata da yayi taqi dagawa sai Angon ya ɗauki wayarsa ya turawa Amaryar tasa saƙon karta-kwana wato (Text Message), cewa:

Na sakeki saki ɗaya.

Kafin kace komai! ko minti daya ba’a qara ba sai ga wadannan Ƙawayen amaryar da suka nace se am basu kudim siyan baki Naira dubu dari biyu 200,000 sun buɗe ƙofar dakin kuwa cikin sauqi kowa ta gudu gidansu suqaf-suqaf suna masu rufe fusakunsu suka bar Amarya da Sallallami cikin baƙin ciki.

Note! Iyaye da sauran Al’umma sai a kula a kiyaye a ɗauki darasi kan wannan kudin siyan bakin na al’ada wanda ba addini yazo da hakan ba.

Ra’ayoyin mutane kan cewa da ace sune angon :

Ga abinda wani bawan allah ya fada kan cewa da ace shine angon, wannan da alama yana nufin ze iya kai duka idan sukaci gaba da jayayya da qawayen amaryar.
Wannan shima ya fadi irin nasa ra’ayin
Tofa da alama wannan shi dai ya dage seya kai hannu, to allah ya kyauta.
Nima ga irin nawa ra’ayin.
Tofa ga wani me gaba dayanan abinda ya furta kan irin nasa tunanin.
Wannan haka yake malama.

To Allah dai ya kyauta ya kuma kiyaye gaba.

THANK YOU FOR VISITING OUR SITE HAUSATALENT.

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button