News

Ku kalli bidiyon yadda wani gini ya ruftowa mutane yau a lagos.

Kawo har izuwa yanzu ba’a gama sanin adadin wadanda suka makale a cikin tarin kasar ginin daya rufto ba.

Ma’aikatan ceton lafiya sun yi kokari sunyi iya bakin kokarin su sun yi aiki cikin dare domin neman masu sauran numfashi wadanda basu mutu ba bayan da wani bene mai hawa ashirin da biyu 22 ya ruguje gaba dayansa a jihar Lagos yayin da ake aikin gininsa.

Kawo yanzu an gano mutum goma sha biyar 15 daga bangorayen ginin kuma daga cikinsu shida har zuwa lahira sun mutu yayin da tara kuma suka jikkata sosaii.

An turawa da masu aikin ceton ran da motar da ke kwashe bangori wato katafila zuwa wurin da al’amarin ya faru kuma masu aikin ceton da wasu mutanenmazauna yankin na neman masu sauran numfashin karkashin baraguzan da basu mutu ba da kuma wadanda suka mutum ma.

Har zuwa yanzu an gano mutun hudu 4 masu sauran numfashi wadanda basu rigamu gidan gaskiya ba.

Tun da farko hotona daga wurin da al’amarin ya kasance sun nuna cunkoson jama’a sosai kusa da babban tarin takarcen daya zubowa victims din.

Wannan shine ainahin bidiyon yanda gidan ya rufta

Har yanzu ba’a fayyace dalili ko kuma abin da ya janyo rugujewar ginin ba da kuma adadin mutanen da suka makale a karkashin ginin ba.

A halin da ake ciki yanzu, gwamnatin jihar ta lagos ta bayar da umarnin gudanar da da duk wani bincike kan rugujewar benen kuma ta yi alkawarin bayyana rahoton ga jama’a dazarar an kammala binciken.

Mai bawa mai girma shugaban kasa shawara na musaman kan harkokin manema labarai Femi Adesina, ya ce: shugaban kasaryana me jajanta wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu.

Ya kuma kara da cewa Shugaban qasa Baba Buhari ya umarci hukumomi da su kara kokari wajen ceto wadanda suka makale cikin ginin.

Benen ya rufta ne da misalin karfe biyu da mintuna arba’in 2:45 na rana a unguwar Ikoyi ta masu ido da kwalli dake garin Lagos.

Kamfanin Fourscore ne yake gudanar da aikin ginin wanda ya ke da tarin ayyuka a Birtaniya da Amurka da Afrika ta Kudu da kuma wasu sassan kasar Najeriya daban.

Wani ma’aikacin ginin Eric Tetteh, mai shekara arba’in da daya 41, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa tawagarsa sun dade suna jiran wani injin tona kasa ya isa wurin lokacin da ginin ya rufta amma shuru yaqi qarasowa.

Ni da dan uwana mun tsere, amma akwai sauran mutane a ciki da yawa kimanin mutum dari 100, amma har yanzu ko rabinsu ba’a tono daga cikin wannan ginin daya rufto ba.

Wani ganau ba jiyau ba wanda abin ya faru a gaban idonsa wanda yake aiki a ofis na wani ginin da ke kusa da wanda ya ruguje ya shaida mana cewa ya ji wata irin kara me babban sauti sosaii, ya leka ta tagarsa daga cikin ofshin nasa kuma ya ga ginin yana gangarowa kasa akan idonsa.

Sai dai a wata cewar kamfanin dillancin labarai na AP, mataimakin gwamnan jihar Lagos Femi Hamzat ya gana da mutanen da suka fusata wadanda ke zargin mahukunta wadanda zasu bada temakon gaggawa da kin fara aikin ceto cikin aikin nasu da suka saba na gaggawa.

Wani ganau wanda lamarin ya faru a gaban idanun sa ya ce ya ga lokacin da ginin yake rugujewa.

An samu rugujewar gine-gine da dama masu yawa a jihar Lagos a ‘yan shekaru nan da suka gabata.

A shekarar dubu biyu da goma sha tara 2019, mutum goma 10 ne suka mutu bayan da wata makaranta ta ruguje a jihar shima kwanakin baya wanda har yanxu ba’a gano dalilin rugujewar makarantar ba.

A shekarar dubu biyu da goma sha hudu 2014, wani bena mai hawa shida 6 ya rufta lokacin da wani mashahuran mai yin bushara da magoya bayansa suke ibada, yayin da kimanin mutum dari da goma sha shida 116 ne suka rasa rayukansu a cikin wannan gidan bautar.

Sau da yawa ana sukar ka’idojin gine-gine kuma a baya baya nan ma hukumomin jihar Lagos sun kaddamar da wani sabon tsari na inganta takardun shaida kan kamfanonin da xasu dinga gine-gine a fadin jahar ta Lagos.

THANK YOU FOR VISITING OUR SITE HAUSATALENT.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button