Education

Gwamnati ta ginawa wani gari da babu wanda ya kammala primary makaranta a kano.

A jihar Kano ne da ke cikin arewacin kasar Najeriya, al`ummar garin Shara da ke rayuwa cikin karamar hukumar Sumaila sun kwana suna murna kan ginin makarantar primary da gwamnatin tayi musu sakamakon gina mata makarantar furamare da gwamnati ta yi.

Ana da akalla mutum kimanin dubu uku 3000 da suke rayuwa a cikin garin, amma gaba dayan su babu ko da mutum daya da ya kammala karatun furamare saboda wahalhalun da suke fuskanta wajen zuwa wata makaranta da ke nesa da garin nasu wanda hakan yasa gwamnatin taga ya cancanci data temaka ta ginawa al’ummar wannan gari makarantar primary wacce batayi nesa da mutanen cikin garin ba.

Kungiyar bunkasa fasahar sadarwa da cigaban al`umma, wato CITAD ita ce ta taimaka ta hanyar bibiyar mahukunta wajen ganin an samarwa da al’ummar garin makarantar.

Daliban dake makarantar furamaren garin na Shara sun cika da farin cikin samun sabbin ajujuwan karatu guda biyu da ofishin hedimasta, bayan sun shafe shekaru suna daukar karatu a gindin wata bishiya.

Mallam Muhammad Labiru Musa shi ne shugaban kungiyar iyayen yara da malaman makaranta ta Shara wato PTA, ya shaida wa gidan jaridar mu da cewa rashin irin wannan daddadan yanayin na karatu na cikin dalilan da suka hana al`ummar garin mai kimanin mutum fiye da dubu uku 3, 000 da suke rayuwa a garin yin karatun zamani, don haka babu ko da mutum daya da ya kammala furamare cikin wannan gari.

Malam Muhammadu. Yace:

Tun lokacin da muke kananan yara akwai wani gari can a bangaren kudu da mu mai suna Matigwai, akwai jeji da kuma kwari dake addabar mu idan damuna ta zo babban mutum bai isa haurawa ba saboda irin birai kai har da su ungulu ma sun isa hana ka zuwa makarantar wanda hakan yana daya daga cikin manya-manyan dalilan da suka hana al’ummar kammala karatun zamani.

Shi ma Malam Kabiru Umar Sitti, wanda shi ne malami daya tilo da ake da shi a garin na Shara da yake koyar da karatun a gindin bishiya, ya shaida mana cewa a wasu lokutan idan yara na daukar karatu a gindin bishiya, haka za a zo ana sissikar kaikayi ko hatsi wanda dole take sanyawa yaran su hakura da karatun, amma yanzu wadannan ajujuwan da aka yi musu za su qara bayar da kwarin gwiwar ci gaba da koyar da daliban.

Tuni dai wasu daga cikin daliban suka fara jin cewa burinsu na rayuwa zai cika tunda an gina musu makarantar koyan ilimin zamani, inda wata daliba mai suna Zahira Musa ta ce a baya suna karatu a gindin bishiya ne, kuma da zarar damuna ta tsaya sai dai hakuri saboda babu damar gudanar da karatun ruwa ya hana. Ta ce wadannan ajujuwa da aka gina musu sun ba ta kwarin gwiwar zage dantse har sai burinta ya cika na zama jami’ar kiwon lafiya nan gaba in allah ya yarda.

Cibiyar bunkusa fasahar nan ta sadarwa da cigaban al`umma, wato CITAD, ita ce ta yi ta kai kukan al’ummar garin na Shara dake qaramar hukumar Sumaila wajen nuna wa duniya matsalar da ke damun al`ummar Shara ta rashin makaranta ta hanyar bin hukomomin da shuwagabannin siyasa, har a karshe maganar ta kai ga share musu hawaye yanzu haka har an gina musu makarantar.

Shugaban karamar hukumar Sumaila, wanda mai taimaka masa, Alhaji Nasiru Ibrahim Sitti, ya tabbatarwa da cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya ji korafin mutanen garin. Za kuma a kai musu kayan koyo da koyarwa da kujeru har da karin malamai ma domin inganta wannan makaranta.

A jihohin dake arewacin Najeriya da dama, akwai irin wannan al`ummar masu yawan gaske, wadanda abu kalilan mahukunta za su yi su sauya musu rayuwa. Kididdiga ta nuna yawancin yara mata da maza ba sa samun damar yin ilimin boko a arewacin kadar Najeriya, ko dai saboda rashin wadatar makarantu, ko rashin kwararrun malamai ko kuma cire yara mata a yi musu aure cikin kankantar shekaru wato Early Marriage.

THANK YOU FOR VISITING OUR SITE HAUSATALENT.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button