News

Ku kalli yadda aka kashe dan fashin dajinnan Damina.

Har yanzu bayanai nata ƙara fitowa fili kan maganar damina, suna bayyana a kan wani faɗan cikin gida da aka samu tsakanin ‘yan fashin daji, wanda ya zama sanadin mutuwar wasu daga cikinsu a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin kasar Najeriya.

Wadansu mutane mazauna yankin wadanda suke da masaniyar abubuwan da suka faru sun shaida mana yadda wani rikici daya faru tsakanin ‘yan fashin dajin ya zama sanadin ajalin wani ƙasurgumin ɗan fashin da ya addabi wasu bagarori da sassan jihar da hare-hare da kuma satar mutane don neman kuɗin fansa wato KIDNAPPING.

Rahotanni da dama sun ce cikin laifukan da ake zargin ‘dan fashin dajin wato Damina, da aikatawa kafin a kashe shi, sun hada d har da ƙona wata mata da ranta ba tare data mutu ba.

Mallam Nuhu Ɗan Sadau, wani mutumin garin Ɗan Sadau ne dake rayuwa a cikin garin mai maƙwabtaka da dajin da ‘yan fashin ke samun mafaka, ya shaida mana da cewa lamarin ya faru ne makonni uku da suka gabata.

Sannan kuma yace:

Yanzu Allah ya taimake mu duk inda aka ji fashin ‘yan bindiga daya, biyu, zuwa uku ya faru to insha Allah sai ka ji wani abu ya faru tsakaninsu suna ta kashe a junansu,

Ya ce:

A baya-baya nan cikun ‘yan makonni mun samu raguwar yan fashin daji fiye da kimanin guda dari da hamsin 150 wajen rabon ganima da wasu abubuwa, sai su kama fada wanda daman hakan babbar halayyace da take yawan faruwa tsakanin yan ta’adda, su kashe junansu, shi ya kawo labarin da kuke ji cewa Dogon Gide ya kashe Damina,

Zahirin Yadda aka kashe Damina

A cikin bayanan da aka samu kan kashe-kashen baya-bayan nan na ‘yan fashin daji, labarin kisan da aka yiwa Damina da yaransa sama da kimanin guda dari 100 ya fi jan hankalin jama’a sosai.

Bayanai da dama sun kuma ce fadan da suka yi na da nasaba ne da satar shanun Dogo Gide da akayi wanda ake zargin Damina ya yi a yankin da Dogo Gide yake da tasiri.

Mallam Nuhu Ɗan Sadau ya ce:

“Damina ya samu labarin Dogo Gide ya fita daga yankin da yake zaune, sai Damina ya saci hanya ya shiga hurumin Dogo Gide, ya kwashi shanu masu yawan gaske na Dogo Gide kuma ya kori dukkanin al’ummar da ke zama a wurin“.

Wadannan mutane su suka hada shi da Dogo Gide har ya kore shi daga yankin da yake zaune a ciki, saboda haka yanzu su ma sun bar wurin kuma sai ya ga yadda za su debi amfanin gona, idan suna so sai sun ba da zunzurutin kudi kimanin Naira miliyan shida 6,000,000.00″

A irin yadda bayanan suka kuma ce sai da Damina ya sa wa mutanen garin haraji, ya kuma wakilta wadanda za a bai wa kudi har miliyan shidan daya nema a hannunsu kafin su ciri amfanin gonakin nasu.

Sun kuma ce again bayan komawarsa sai Dogo Gide ya samu labari kuma ya bi sahu, shi ma ya kashe na kashewa, ya kwaso shanunsa da aka sace kuma shi ma ya sato na Damina.

Mallam Nuhu Ɗan Sadau ya kara da cewa:

An sace masa shanu fiye da guda dari 100 shima, shi kuma ya sato sama da guda dari uku 300, to shi ne kuma Damina ya shirya shina daya sake biyo baya shima, shi kuma Dogo Gide da ya yaki shiryayyen dan fashin daji ne ya shirya masa wani irin harin kwantar bauna, ko da zai biyo da tawagarsa sai da ya shigo tsakiyar dajin da ake kira Farin Ruwa da ke kusa da garin Ruwan Tofa.

A wannan daji suka yi ba-ta-kashi, suka kashe mafi yawan yaran da Damina ya zo da su.”

A cewarsa:

Ni na ga wanda ya ga bindigar Damina, da babur dinsa da jakar makaminsa domin a kai su wani kauye da ake kira Chilinda.

Bayana da yawa sun ce Damina ya tafi da raunuka sosai bawai a gurin yakin ya mutu ba kuma an samu labarin ya bulla a kauyen Farin Ruwa inda a nan ya gamu da ajalinsa bayan ‘yan kato da gora sun sanar da mazauna kauyen wadanda suka taru suka sassare shi.

Sai dai kawo yanzu babu wata majiya mai zaman kanta me karfi da ta tabattar da wannan labari kuma mahukunta har yanzu ba su ce komai ba a kan wannan batun.

Amma a baya bayan nan an kashe rikakkun ‘yan fashin daji, cikinsu har da Nasiru Kachalla da Auwal Daudawa da dai sauran manya-manyan’ yan ta’adda.

THANK YOU FOR VISITING OUR SITE HAUSATALENT.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button