News

An samu fashewar tankar mai a Freetown dake Salo.

Akalla sama da mutane tamanin da hudu 84 ne suka mutu bayan wata mummunar fashewar wata babbar tankar man fetir da ta yi taho-mu-gama da wata babbar mota a Freetown, babban birnin Saliyo.

Man fetur ya kwarara sosai akan titin da akayi wannan arangamar kafin wuta ta tashi inda ta mamaye mutanen da ke kusa da wajen tare da konewar motoci da dama a wata mahadar hanya mai cike da jama’a.

Hotunan da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda wuta ke ci a wurin sosai, al’amarin ya faru ne yayin da man da ke ci da wuta ke bazuwa, inda motoci da dama suka ƙone tare da haddasa wata fashewar ta abubuwa da dama a wurin da accident din ya faru.

Fashewar dai ta afku ne da yammacin ranar Juma’a jiya kenan lokacin da mutane suke tsaka da hada-hadar kasuwanci.

Julius Maada Bio Shugaban kasar ta Sierra Leon wadda akafi sani da Saliyo ya ce:

ya yi matukar damuwa sosai bisa yadda wannan musiba ko kuma bala’i na wuta da kuma rasa rayukan jama’a ya kasance“.

A saqon daya wallafa a Twitter

ya ce:

Gwamnatinsa za tayi dukkan wani abin da ya dace domin taimaka wa iyalan mutanen da lamarin ya rutsa da su da yardar Allah“.

Magajin birnin na Freetown Yvonne Aki-Sawyerr shima ya bayyana ganin hotuna masu tayar da hankalin Al’umma sosaii sannan kuma ya ce: anata jita-jitan fiye da kimanin mutum dari 100 sun rasa rayukansu“.

An bayar da rahoton da gawarwakin mutane fiye da guda casa’in 90 aka miqasu izuwa mutuware sannan kuma ana yi wa fiye da kimanin aqalla mutum dari 100 magani a asibitoci da cibiyoyin kula da lafiya da ke birnin na Freetown.

Wani rahoton na daban shima ya ce wata motar bos cike itama da mutane ta kone kurmus, yayin da wasu shaguna da kasuwar da ke kusa da inda lamarin ya faru suka kone suma harda kayan dake cikin su.

Brima Bureh Sesay, shugaban hukumar kai daukin gaggawa ta Sierre Leone, ya shaida wa kafafen yada labaran kasar cewa:

Wannan lamarin wani babban bala’i ne dabe taba faruwa ba a kasar Sierra Leon ko kuma makamancin sa“.

THANK YOU FOR VISITING OUR SITE HAUSATALENT.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button