News

‘Yan bindiga dake yankin Nijar sun qara kashe sojoji 10

Wasu qasurgumayen ‘yan bindiga dauke da mugwayen makamai sun qara hallaka sojojin Jamhuriyar Nijar kimanin guda goma 10, yayin wani hari da suka kai wani sansanin soji dake yankin.

Ana ta fargbar cewa karin wasu sojojin guda tara sun yi batan dabo yayin harin da yan bindigar da ake zargin masu iqirarin jihadi ne suka kai kauyen Anzourou.

Ma’aikatar Jamhuriyyar Nijar ta ce:

Maharan sun isa ne a kan motoci da babura masu yawa, yayin da suka bude wa sojojin da ke tsaron jama’ar garin wuta fafafa ba kama qafar yaro.

Wannan na faruwa ne yayin da ake zaman makokin akalla kimanin sojojin kasar guda 70 da masu ikirarin jihadi suka kashe a iyakar kasar da Mali da Burkina Faso.

Ranar Juma’ar da ta wuce ne Jamhuriyyar Nijar ta ayyana zaman makoki na kwanaki biyu 2 daga yau Juma’a bayan da wasu da ake zargi masu ikirarin jihadi ne sun kashe kimanin aqalla mutum saba’in 70.

Harin dai ya faru ne a kudu maso yammacin ƙasar wadda take kan iyakar Nijar ɗin da kuma Mali.

Cikin waɗanda harin ya rutsa da su har da wani magajin gari da kuma shugaban wata rundunar sa, kamar yadda gwamnatin ƙasar ta bayyana.

Tace:

Babu wata ƙungiya da ta fito ta ɗauki nauyin kai wannan harin anma rasa ‘yan wacce kungiyane keep the kuma daga ina suke ko kuma sanin wanda ya dauki nayin su ya turo su dasu aikata wannan mummunan abin. Waɗanda suka kai harin sun tsere ta iyakar ƙasar da kuma Mali inda rahotanni da dama suka ce sun ɗauke gawargwakin ƴan uwansu da aka kashe.

Ma’aikatar harkokin cikin gida dake Jamhuriyyar Nijar ɗin ta kuma ce ‘yan bindiga din sun yiwa wani ayarin mutane ƙarƙashin jagorancin Magajin Garin Banibangou kwantar ɓauna a wani ƙauye da ke da nisan kilomita 55 daga wurin da lamarin ya faru a Yammacin Tillaberi.

Allah ya kawo mana qarshen wannan ta’addancin da yake faruwa a kasashen mu.

THANK YOU FOR VISITING OUR SITE HAUSATALENT.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button