Education

Neco: Daliban kano na rashin tabbas kan bashin gwamnati

Sama da kimanin ɗalibai guda dubu 80,000 ne ke cikin barazanar rasa gurbin karatu a makarantun gaba da sakandare, sakamakon maƙalewar jarrabawarsu ta NECO da sukayi wannan shekarar, wanda har yanzu gwamnatin jihar ta kasa biyan bashin da ke kanta, ballantana ta biyawa daliban kudin jarrabawarsu.

Wannan yanayin da ɗaliban suka tsinci kansu na da alaƙa da gazawar gwamnatin jihar na biyan kuɗaɗen da hukumar shirya jarrabawar kammala sakandare ta Najeriya wato NECO ke binta wanda ta kasa biyanta.

Kashi 70% cikin 100% na ɗaliban da suka rubuta jarrabawar NECO ta wannan shekarar da muke ciki 2021, iyayensu ne suka biya musu kuɗin jarrabawar, amma har yanzu babu labarin sakin jarrabawar tasu.

Wannan yanayin da ɗaliban ke ciki ya ja hankali sosai, abin da ya kai ga ƙungiyoyin masu fafutika da kuma jan hankalin gwamnati don ganin yaran ba su rasa wannan gurbin karatun nasu ba.

Jihar Kano na cikin jerin jihohi irin su Adamawa da Niger da Zamfara wanda NECO ta ce tana bi miliyoyin naira na bashin kuɗin jarrabawar ɗalibansu.

Abubuwan da ɗaliban ke cewa akai

Ɗaya daga cikin ɗaliban da wannan lamari ya shafa ya shaida wa BBC cewa suna cikin tasku, domin makarantun gaba da sakandare suna ci gaba da rufe gurbin ɗaukan ɗalibai, a zangon karatun na bana.

Ya ce yana dakon jarrabawar ne domin samun damar shiga jami’ar da ya nema, kuma da alama idan aka ci gaba da fuskantar wannan tsaiko watakila ya rasa damarsa.

Mun yi yunƙurin tuntuɓar makarantar tamu amma sai a ce mu sake haƙuri, ga shi lokacin daukar na sababbin dalibai na wucewa, ban san makomata ba.

Wannan yanayi da ake ciki ya tilasta wa wasu masu fafutikar aike zuwa ga gwamnati, wasiƙar da ke bayani kan halin da ɗaliban ke ciki da kuma neman daukan mataki da gwamnatin ya kamata ta tayi.

Shin me gwamnatin ta ce kan wannan lamari na neco ?

Munyi kokarin ji ta bakin kwamishinan ilimi na jihar Kanon, Sunusi Sa’id Kiru domin jin me ke faruwa, sai dai kuwa hakan bai samu ba.

Amma shugaban wata ƙungiyar farar-hula a Kanon, wato Kwamared Umar Ibrahim Umar ya ce korafe-korafen da suka samu daga ɗalibai da dama a daidai lokacin da jami’o’i ke gab da rufe kofar ɗaukan ɗaliban, ya sa suka tashi haiƙan don ganin gwamnati ta warware wannan matsalar amma sedai abin yaci tura yaqi cinyewa har yanzu.

Kwamared Umar ya ce za su bi duk wani mataki na doka don ganin an saki jarrabawar yaran, waɗanda mafi akasarin su da kansu suka biya kuɗin jarrabawar ta NECO.

BASHIN DA NECO KE BIN GWAMNATIN JIHAR TA KANO.

Rahotanni da dama na cewa hukumar NECO na bin gwamnatin Kano kimanin sama da naira miliyan dari biyar 500,000,000 duk da cewa a makon da ya gabata gwamnati ta shaida cewa ta rage bashin da ake binta da naira miliyan dari 100,000,000 wanda ya rage sauran milayan dari hudu 400,000,000.

Gwamnatin jahar Kano ta alaƙanta hakan da yawan bashin da NECO ke binta da kuma matsalolin matsin tattalin arziki da kuma rashin kuɗaɗen shiga da jahar take fama dashi.

Wannan ba shi ne karo na farko ba da ɗaliban jihar Kano ke shiga cikin irin wannan yanayi, domin kusan kowacce shekara da ake rubuta wannan jarrabawar ba a rasa irin wannan korafin na rike jarrabawar ɗaliban saboda bashi.

A watan April ma an samu kimanin ɗalibai guda dubu ashirin 20,000 da suka rubuta jarrabawar kammala sakandare ta Arabiya da ta fasaha da aka rike jarrabawar su akan bashi.

Haka kuma shima a shekarar da ta gabata, sai da aka rike wa ɗaliban jahar sama da kimanin dubu saba’in 70,000 sakamakon jarrabawarsu, har sai da aka biya NECO bashin da take bi na sama da naira miliyan dari shida da arba’in 640,000,000.

THANK YOU FOR VISITING OUR SITE HAUSATALENT.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button