Politics

Shugaban Qasa zeyi nazari kan batun Nnamdi Kanu

Shugaban Qasar Najeriya Muhammadu Buhari ya ce: zai duba sosai yayi nazarin buƙatar da ya kira mai girman gaske ta neman ya saki Nnamdi Kanu wadda ƙungiyar dattawan al’ummar yankunan Ibo suka gabatar masa.

Mister Kanu shugaban tawagar inyamurai wanda ake zargi da aikata ta’addanci a gaban kotu, na hannun ‘yan sandan farin kaya na DSS sakamakon gwagwarmayar da yake yi kan neman kafa ƙasar Biafra a kudancin Najeriya ƙarƙashin ƙungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) da aka haramta.

Shugaba Muhammad Buhari ya bayyana hakan ne yayin da yake karɓar baƙuncin dattawan a fadarsa da ke Abuja ranar Juma’a ƙarƙashin jagorancin tsohon Ministan Sufurin Jirgin Sama Mbazulike Amaechi.

A wata cewar da Buhari cikin wata sanarwa da Femi Adesina ya fitar, yace :

Kun nemi abu mai matuƙar girma a wajena a matsayina na shugaban wannan ƙasa. Tasirin buƙatar taku na da girma sosai,”

Ya ƙara da cewa buƙatar da dattijan qasar suka nema a gurinsa ta saɓa wa tanadin tsarin kundin mulki da ya fayyace tsarin shugabanci tsakanin gwamnati da ɓangaren shari’a.

Sai ya qara da cewa dai buƙatar da suka gabatar mai girma ce sosai amma zan yi dogon nazari a kanta,”

AFRICA TA KUDU TA SHAHARA WAJEN AIKATA MANYA-MANYAN LAIFUKA.

Alƙaluman aikata laifuka na baya-bayan nan da aka fitar a yankin Afirka ta Kudu ya nuna cewa abu ne mai muni kamar na baya, a cewar Ministan Harkokin ‘Yan Sanda Bheki Cele.

Kamar yadda shafin manhajar Twitter na gwamnatin tarayya ya bayyana cewa, ministan ya ce bayanan na watan June zuwa September sun nuna cewa Afirka ta Kudu ” ta kasance daya daga cikin manya-manyan gawurtattun ƙasashen duniya a yankin Africa wajen aikata manyan laifuka”.

A cewar Ministan Harkokin ‘yan sandan yace: aikata kisan kai ya ƙaru da kashi 21 cikin 100 idan aka kwatanta da irin wannan lokacin na shekarar da ta gabata.

Dangane da cin zarafi ta hanyar lalata kuwa, ya ce:

An yi wa kimanin sama da yara mata dubu tara da dari biyar 9,500 fyaɗe cikin wata uku kacal abin da ke nufin duk awa ɗaya ana aikata fyaɗe sau huɗu a yankin. Lamarin ya ƙaru da kashi 7 kenan cikin 100 wanda jimillar sa ya koma kashi ashirin da takwas 28.

A cewar Mr. Cele ya nuna cewa :

Wajibi ne a ƙara ƙoƙari wajen tabbatar da cewa an kare rayukan ‘yan Afirka ta Kudu,

KIMANIN SAMA DA ‘YAN MATA GUDA 7 NE SUKA RASU SAKAMAKON WANI HADARIN JIRGIN RUWA DA AKAYI A JIGAWA STATE

Rahotanni sosai daga Jihar Jigawa a arewacin Najeriya da suka jewa shugaban qasa, na nuna cewa wasu ‘yan mata guda bakwai 7 sun rasa rayukansu sun rigamu gidan gaskiya bayan da wani jirgin kwale-kwale da suke tafiya a ciki ya kife ranar Alhamis da daddare.

Lamarin dai ya faru ne a daidai lokacin da suke kokarinsu na suga sun tsallaka wani kogi a kan hanyarsu ta dawowa daga taron wani Maulidi da aka gabatar a garin Gasanya.

Bayanai da yawa sun ce jirgin na dauke da mutum kimanin goma sha biyu 12 ne lokacin da ya kife a cikin kogin wanda ke tsakanin kananan hukumomin Auyo da kuma Kafin Hausa, inda bakwai suka rasu, biyar suka tsallake rijiya da baya. Allah ya gafarta musu ameen.

Mutanen dai na kan hanyarsu ne ta komawa garinsu na Gafasa da ke qaramar Hukumar Kafin Hausa daga Gasanya na karamar hukumar Auyo.

Malam Mikail Jibril daya ne daga cikin iyayen wa danda suka rasu, kuma ya shaida wa babban gidan jaridar BBC Hausa cewa shekarun ‘yan matan in average ba zai wuce shekara goma sha daya 11 zuwa goma sha biyu 12.

Mai garin na Gafasa Alhaji Adamu Abdullahi ya ce tuni aka yi jana’izarsu.

A watan May na wannan shekarar da muke ciki wato 2021, mutum fiye da dari 100 ne suka rasa rayukansu sakamakon irin wannan hatsarin na jirgin ruwa da ya afku kusa da garin Warah na Jihar Kebbi duk a yankin na arewa maso yammacin Najeriya shi kuma.

Allah yasa ya kyauta namu zuwan ameen.

THANK YOU FOR VISITING OUR SITE HAUSATALENT.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button