Health

Tsarin iyali na maza da kuma yadda akeyinsa.

(Tsarin iyali) Tsarin iyali wata hanya ce da ake bi wajen ganin an daqilar da samun jaririn da ba’a shirya haihuwar sa ba da wuri.

Akwai hanyoyi da dama da ‘ya ‘ya maza za su iya bi domin ganin sun kare kansu daga samun jaririn da ba a shirya haifarsa ba da wuri.

Tsarin iyali.

Yanxu zamu fara da hanyoyi guda 3 uku da kuka fi sani ko kuma sabawa dasu kamar haka:

Kwaroron roba na maza (kwandem).

Yin amfani da kwaroron roba dake bada kariya wajen yaki da cuta me karya garkuwar jiki itama wata sananniyar hanya ce da maza ke amfani da shi domin kare kai daga yin cikin da ba a shirya ma sa ba a zuwa wani lokaci.

Ana ganin kamar amfani da kwaroron roba na ba da kariya daga daukar ciki da kashi casa’in da takwas 98% a cikin kaso dari 100%, kuma ita ce kadai hanya daya callin cal, da ake ganin na bayar da kariya daga kamuwa da cutukkan da ake dauka ta jima’i.

Sannan Hukumar Lafiya ta Duniya wato World Health Organisation (WHO) ta bada shawarar sayan kwaroron roba daga kamfanonin da suke da ke kima, da kuma wadanda asusun Majalisar Dinkin Duniya ya san da su kuma ta yadda dasu.

Rashin gamsuwa yayin jima’i.

Sassaukar hanya ce amma kuma ba ta da tabbas, saboda kashi ashirin da bakwai 27% cikin kaso dari 100% na maza wannan lokacin na kubuce musu, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana yayin wani jawabi data gabatar.

Hukumar lafiya ta Birtaniya NHS, har yanzu ita ba ta aminta da wannan hanya a matsayin ta tsarin iyali ko takaita haihuwa ba ko kuma kaucewa daukar ciki ba.

Dalilin ta kuwa naqin yadda da wannan tsarin shi ne, ruwan maniyyi wato sperm ka iya fita gabannin lokacin gamsuwa yayin jima’in, wanda dan kankani ne daman ke samun damar shiga mahaifa tare da zama aciki ya samar abinda akeso.

Sai dai duk da haka, Moussa Diabaté kwararrene a fannin lafiyar kwayayen haihuwa a Qasar Senegal, ya bayyana cewa matakin amfani da kwaroron roba, da janye gabanka gabannin fitar maniyyi na da tabbas, domin hanya ce da aka dade ana amfani da ita a kasar, kuma kwalliya na biyan kudin sabulu.

Sai dai ga Dr. Mobile Kampanga, shima kwararren likitan maza ne a Qasar Congo, ya ce: ba wannan ce hanyar da ya ke bai wa abokan huldarsa shawarar amfani da ita ba.

Hakikanin gaskiya, tsohuwar hanyar da ake amfani da ita ba ta aiki, sakamakon yawancin mazan da suka yi amfani da ita sun bada bayanai mabambanta babu wani tsayayyen bayani akai.

Wasu daga ciki sun ce ba za su kara amfani da ita ba, yayin da wasu suka ce sam ba za su gwada yin hakan ba su kuma“.

Ma’aurata, ko abokan rayuwa ka iya sake yin jima’i wani lokacin a karo na biyu, kuma ta yiwu wani daga cikin maniyyin namijin ya makale a wani wajen, sai a lokacin saduwa zai shiga mahaifar mace daga nan kuma sai ciki ya shiga.

Aikin Tiyata ga ‘yaya maza.

Wannan wata hanya ce ta da ake yin tiyata wacce ta hada da yanke hanyar da maniyyi ke bi wajen fita, tare da toshe wajen da yake biyowa.

Yawanci idan za a yi wa mutum irin wannan tiyatar ana yi wa mutum allurar da ke dakatar da wani bangare na jiki, ma’ana mutum zai kasance idonsa a bude amma ba zai taba jin zafi ko sanin abin da ke faruwa dashi ba, kuma aikin na daukar tsawon mintina 15 kacal ba yawa.

Kamar yadda shafin hukumar lafiya na Birtaniya NHS ta tabbatar, tace amfani da hanyar tiyata kwalliya na biyan kudin sabulu da kusan kashi casa’in da tara 99%.

Ana kallon wannan hanya da dawwamammiya, duk da dai ana iya komawa a sake mayar da komai yadda yake idan bukatar hakan ta taso.

Sai dai abin lura a nan shi ne ba a cika yin amfani da wannan hanyar ba a yankin nahiyar Afirka, kamar yadda Dr. Kampanga ya bayyana cewa yawancin maza ba su yadda da wannan aikin tiyata ba.

Ya kara da cewa cikin shekaru ashirin da bakwai 27 da ya dauka yana aiki a matsayin likitan fida da ya shafi mafitsarar maza, sau 10 kacal ya taba yin aikin tiyatar wanda hakan shine ya tabbatar masa da cewa maza basu yadda da a dinga yi musu wannan tiyatar ba, Maza qalilan ke iya yadda da hakan.

Yawancin maza na fakewa da abinda addini ke cewa domin kaucewa gabatar da aikin, yayin da wasu kuma ke kaucewa hadarin aikinne kawai. Don haka ne suke tilastawa mata shan maganin tsarin iyali, domin su su kubuta daga waccan tiyatar.’

Shin wadanne hanyoyi ake amfani da su na tsarin iyali a nahiyar Afrika?

A iya cewa baki daya a nahiyar Afirka, maza ba sa amfani da hanyoyin tsarin iyali ko dai na shan kwayar magani ko amfani da kwaroron roba, sai tsiraru daga cikin mutanen nahiyar ne ke bin hanyoyin da jami’an lafiya suka bada shawara domin kaucewa yin cikin da ba a shirya ma sa ba wanda hakan yasa qananun yara sukafi yawa a nahiyar ta Africa.

Ana ganin hanyoyin kare kai daga daukar cikin da ba’a shirya masa ba, ya dogara ne baki daya akan Mata, ko dai shan kwayar magani, ko sanya zaren da ke toshe bakin mahaifa, domin hana daukar ciki da kidayar lokacin jinin al’ada, ko yin allura, ko kuma maganin gargajiya da dai sauransu.

Dr. Madina Ndoye, kwararriyar likitar mata a asibin Grand-Yoff dake birnin Dakar na kasar Senegal, ta ce:

yawancin bayanin da maza ke yi dan kubuta daga wannan aikin yana da alaka ne da addini da kuma al’ada kan batun tsarin iyali, domin haka ne suke fakewa, tare da nade hannu sai dai mata ne kadai suke yin tsarin iyalin.

Wani mutum mai suna Bolozi Kalombo mazaunin birnin Kinshasa ya shaida mana cewa ya haramtawa matarsa shan maganin hana daukar ciki.

Saboda ina son ganin mata na yin abu da gaske ba kulumboto ba, sannan kuma jikinsu na sauyawa idan suna amfani da magani ko allura da sauran hanyoyin tsarin iyali.

Wannan dalilin ne ya sanya ni da matata ba mu taba yin amfani da duk wani nau’in tsarin iyali ba, saboda ni mabiyin addinin Kirista ne kuma littafin mu mai tsarki ya fayyace mana abu mai kyau da mara kyau a cewarsa.

Kawo yanzu ana ci gaba da bincike kan maganin tsarin iyali na maza.

Har yanzu ana ci gaba da gwaji da nazari kan hanyoyin da dama na tsarin iyali a sassa daban-daban na duniya. Wato amfani da kwayar magani ko sauyin jiki na Homourns (CHM).

Sama da shekaru hamsin da suka wuce 50 kenan da masana kimiyya suka duqufa suna ta nazari, sai dai har yanzu kwalliya ta kasa biyan kudin sabulu, kuma babu ko guda daya da aka fitar a kasuwa har yau.

Wani nazari da hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi a shekarun baya daga 1990 zuwa 1996, ya nuna tasirin da allurar CHM ta sati-sati mai adadin mili giram dari biyu 200 ga maza za ta yi gare su.

Shin menene ya sa ake jiran tsammani kan maganin tsarin iyali na maza?

A wani bincike da China ta gudanar har sau biyu, a shekarun 2003 zuwa 2009, ya yi bayani kan ingancin yi wa maza tsarin iyali ta hanyar allura daya cikin watanni hudu wacce mafi akasarin mutane ita ake amfani da ita.

Dr. Mobile Kampanga, ya shaida mana cewa likitoci ba sa bayar da shawarar yin allurar saboda illarta da ta ke yi a cikin sauyin halittar dan adam, da rashin tabbas ga wanda aka yi wa.

Wata hanya da maza ke amfani da ita wajen qididdige iyali ita ce hanyar sanya matsattsen duros, na akalla sa’o’i 15 a kowacce rana na tsahon watanni uku, da nufin dumama maniyyin yadda ba zai yi tasirin fitar da kwan haihuwa ba.

Wannan tsari ya nuna tasiri kan mazaje kimanin hamsin da daya 51 da akai gwaji akan su, daya daga cikin su ne kadai aka samu kuskure ciki ya shiga, shi ma din bai yi amfani da tsarin yadda ya dace bane, kamar yadda kungiyar likitocin fidar mafitsara na kasar Faransa suka bayyana.

Yin allura mai nau’in mai.

Wata kungiya mai zaman kan ta a Qasar Amurka, me suna Parsemus Foundation ta dade tana nazari akan allurar da ake yi wa ‘ya’yan maraina, wadda a hankali cikin shekaru take yin tasiri kan toshe hanyar da maniyyi ke fita.

Hanya ce mai sauki kuma marar hadari da za a iya sake yin wata allurar domin narkar da toshewar bayan da tosheta da akayi a baya domin dakatar da lamarin, kamar yadda shima kungiyar likitocin fidar mafitsara na kasar Faransa suka bayyana.

Kawo izuwa yanzu an yi gwajin allurar akan Birrai da zomaye, kuma alamu sun nuna tasirinta sosai, amma sai dai har yanzu ba a samu cikakken sakamako kan sake yin allurar da kuma narkar da toshewar hanyar da miniyyin ke fita ba.

Maganin da ake shaka wanda bana sha ba.

Tun a cikin shekara ta dubu biyu da sha shida 2016 masu bincike na nahiyar Birtaniya suka duqufa kan nazari, domin nemo maganin tsarin iyali na shaka, da zai yi tasirin rage karfin maniyyi.

Sun gabatar da yin aikin ne wajen yin hadin gwiwa tare da jami’ar Aveiro, ta Portugal, a wani bangare na binciken shekaru uku 3 da aka warewa kimanin Yuro dubu dari da casa’in da hudu £194,000 domin aiwatar da binciken, domin gano illar da maganin shakar kan iya yi wa kwayoyin halittar dan adam, da yadda za su kayyade maniyyin da namiji ke fitarwa.

THANK YOU FOR VISITING OUR SITE HAUSATALENT.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button