News

NLC sunce basu yarda da janye tallafin mai ba.

NLC qungiyar ‘yan kwadago ta Najeriya ta yi watsi da shirin gwamnatin tarayya na kasar kan janye tallafin man fetur da zatayi wanda zai kai ga ƙara tsadar farashin man fetur din zuwa sabuwar shekara me kamawa 2022.

Kungiyar ta ce ita dai ba za ta yarda ta faɗa gadar zaren da gwamnatin tarayya dake ƙasar ke neman shiryawa mutanen qasar ta ba, yadda ta bayyana a cikin wata sanarwa data gabata mai ɗauke da sa hannun shugaban NLC Ayuba Wabba.

Cmrd Ayuba Wabba ya ce: batun da shugaban qungiyar NNPC Malam Mele Kyari ya yi akan karin farashin man fetur zuwa Naira dari uku da arba’in 340 daga watan February na sabuwar shekara sam ba ta yiwa al’ummar kasar dadi ba.

A cikin sanarwar qungiyar ta ‘yan kwadago dake qasar tayi ta ce tunanin rabawa ƴan kasar ta Najeriya guda miliyan 40,000,000 Naira 5,000 domin rage musu radadin karin farashin na man fetur abin dariya ne sosaiinda ta ce idan aka lissafa kudin da zata rabawa al’ummar qasar ze haura na tallafin man fetur din da ake bayarwa a kasar.

Gwamnatin Qasar Najeriya dai ta ce za ta janye tallafin mai gabaki ɗaya acikin tsakiyar sabuwar shekara me kamawa 2022, kuma tana tunanin raba wa ƴan Najeriya kuɗin tallafin domin rage raɗaɗin da tasirin janye tallafin zai haifar ga mutanen qasar.

Amma ƙungiyar kwadagon NLC ta jaddada rashin gamsuwar ta da cire tallafin man inda ta ce zai karawa ‘yan kasar matsin rayuwa sosai.

Haka kuma sanarwar ta ce abin takaici ne ganin cewa qasar Najeriya ce kadai kasa cikin mambobina OPEC da ba ta iya tace man fetirin da ta ke samarwa a cikin gida, sai an fitar da shi sauran kasashen dake ketare sannan ake iya samar da wanda za’ai amfani dashi.

Daga karshe dai Ayyuba Wabba ya ce kamar yadda suka saba yi a kowanne lokaci, suna kira ga gwamnatin tarayya ta duba wasu hanyoyi guda uku da suke ganin ya kamata abi domin kawo sauki kan wannan batun.

  • A rika saukakawa masu sayar da man fetur din da kuma faduwar da darajar Naira take yi ke shafar su, ta hanyar shiryawa sauran kasasahe makwabta wajen amfani da matattun gangunan mansu domin tace man da Najeriya ke samarwa zuwa kasashen qetare.
  • A yi kokarin farfado da matattun gangunan mai guda hudu 4 da Najeriyar ke da su, wanda za su saukaka fitar da man fetur din da kasar ke hakowa, ta hanyar tace shi da sarrafawa a cikin gida.
  • Sannan ya qara da cewa tattara kididdigar yawan man fetur din da ‘yan Najeriya ke amfani da shi kowacce rana, saboda wannan na daga cikin abubuwan da babu ainahin kididdigar yadda ake amfani da shi a kasar.

A karshe kuma sanarwar ta ce matukar ba a dauki matakin ba, tabbas wahalar za ta kare ne iya kan talakan Najeriyar, sakamakon yadda farashin dalar Amurka ya kai kimanin Naira 564.

A shekarar dubu biyu da sha tara 2009 da gwamnatin Najeriya ta cire tallafin mai, kungiyar kwadago NLC ta jagoranci gagarumin jerin-gwano da tayi, don nuna rashin amincewa da shirin gwamnatin kasar na janye tallafi daga harkar mai.

A wancan lokacin manyan hukumomin da suke da hannu da shuni a Najeriya sun ce babu makawa sai an aiwatar da shirin inda suka ce janye talafin nada fa’ida ga jama’ar kasar, saboda zai magance tsada da karancin mai.

Amma kungiyar kwadagon NLC a nata bangaren, ta ce kasashen da ba su da arzikin mai suna daukan matakan tallafa wa al’umomin, don haka ba ta ga dalilin da zai sanya qasa irin Najeriyar ta janye nata tallafin ba duba da yanda basu da wani tsayayyen hanya da suke iya tallafawa mutanen qasar.

A halin yanzu, abinda ake jira a gani shi ne matakin da kungiyar kwadagon za ta dauka akai matukar gwamnatin tarayya ta Najeriya, ta ki amincewa da janye aniyarta ta akan cire tallafin man da takeson tayi.

Allah ya kawo mana sauki cikin lamarin mu ameen.

THANK YOU FOR VISITING OUR SITE HAUSATALENT.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button