Politics

Atiku abubakar yayi tsokaci kan janye tallafin man fetur.

Atiku Abubakar yayi tsokaci kan yunkurin Gwamnatin Najeriya na cire tallafin man fetur daga shekara mai kamawa 2022, kamar yadda asusun IMF ya bukata, ya haifar da mahawara mai zafi a cikin kasar da al’ummar ta. Yayin da wasu ke murna da matakin, duba da irin makudan kudaden da ake zubawa akan tallafin, wasu kuma da dama na sukar matakin saboda illar da suka ce zai yiwa talaka.

Dangane da wannan batun, Ibrahim Malam Goje yaji ta bakin tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma me neman takara a qasar wato Atiku Abubakar, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.

An kunnawa ofishin sanata Barau Jibrin wuta a sanyin safiyar ranar Alhamis din data gabata

Sanata Barau Jibrin na da sagin Sanata Shekarau da ke adawa da tsagin Ganduje, kuma a cikin satin da ya gabata ne kotu ta ba wa tsagin nasu shugabancin jam’iyyar APC a cikin jihar kano.

Da sanyin safiyar ranar Alhamis dinnan data gabata ne wasu ’yan daba masu tada qayar baya dauke da mugwayen. makamai suka kai farmaki ofishin yakin neman zaben gwamna Sanata Barau Jibrin, suka banka masa wuta.

A sakamakon haka ne, tsagin Sanata Shekarau ya shigarwa da kotu Qara ga Shugaban ’Yan Sandan Najeriya tare da zargin mabiya bayan bangaren Ganduje da daukar nauyin harin da aka kaiwa ofishin na Sanata Barau Jibrin wanda kowa ma yake zargin hakan.

Amma a yayin da yake mayar da martani a kan lamarin, kakakin jam’iyyar APC tsagin Ganduje, Ahmed S. Aruwa, ya ce zargin da ake yiwa mabiya bayan me girma gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ba shi da tushe, kuma wani yunquri ne na bata sunan manyan mutane da kuma jam’iyyar baki daya.

Kuma haka zalika, ya ce: “wadansu da ake zargi suna da sa hannu a harin sun dauki lokaci ba sa Najeriyar ma baki daya, ballantana a yi tunanin ko suna da hannu a wannan lamarin.

Ya qara da cewa magoya bayan mai girma gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje, mutane ne masu bin doka da kuma oda, kuma babu wani dalili da zai saka su sanya kansu cikin mugwayen munanan ayyuka irin wannan.

THANK YOU FOR VISITING OUR SITE HAUSATALENT.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button