Politics

Abinda Buhari yace kan batun zaben 2023 da ze gabata

Shugaban Qasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa bai damu da duk wani abu daze faru ba a shekarar 2023 kan batun wanda zai gaje shi ba, a matsayin shugaban ƙasa saboda ya ajiye rahoton komai da komai da dukkanin wani abu da suke da buƙatarsa.

Shugaban ya bayyana hakan ne a hirarsa da wata kafar talabijin ta Channels TV a yammacin Laraba, yana mai bayyana cewa zaɓen shekarar 2023 ba wata matsala ba ce ba kan yadda al’ummar qasar suke ayyanawa“.

Shugaba Buhari ya qara da cewa:

Ban damu da wani wanda zai gaje ni ba, rabu da shi ya zo ko ma wane ne,

Lokacin da yake amsa tambaya kan shin ko me ke zuwa masa a ranshi idan ya ji an ambaci zaɓen 2023 daze gabata, Buhari ya amsa da cewa:Ba matsalata ba ce.

Da aka tambayi shugaban qasarBa ka damu game da wanda zai gaje ka ba? Sai ya ce:

Bar shi ya zo ko ma wane ne niba matsala ta bane. Na tabbata na ajiye rahoton duk wani abu mai muhimmanci daya kamata a nema a wajena. Bai kamata wani ya kira ni ba akan wata shaida dazan kare kainan a gaban kotu akan wani lamarin daya shafi kasa ba, idan ba haka ba kuma mutum zai shiga matsala koma wane.

Buhari shugaban qasar Nigeria ya ce: duk da cewa ba shi da wani ɗan takara da yake goyon baya a jam’iyyar APC mai mulki a yanzu ya gaje shi amma idan ya bayyana shi za a iya halaka shi wannan shine babban dalilin daya saka shugaban yaqi bayyana wanda ze gaje shi. Yace saboda idan har ya sake ya fada to tabbas za’a iya hallaka shi zuwa lahira.

MUN SAUYAWA YAN FASHIN DAJI SUNA ZUWA YAN TA’ADDA SABODA ABINDA SUKA SANI KENAN.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amsa tambayoyin da akayi masa kan batutuwa da dama yayin hirar da ta gabata a fadarsa ta Aso Rock Villa (Federal Government House), ciki har da matsalar ‘yan fashin daji na yankin arewa maso yamma da suka takurawa al’ ummar yankin.

Sai dai har izuwa yanzu babu wata sanarwa da take nuna cewa gwamnatin ta ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda a hukumance tun bayan da Ministan Shari’a Abubakar Malami ya nemi kotu da ta basu damar yin hakan duk da cewa a lokacin kotun ta amince da buƙatar gwamnatin.

FEDERAL GOVERNMENT TACE BAZATA SAKI NNAMDI KANU BA

‘Yan satittikan bayan alƙawarin da ya yi wa dattawan al’ummar Ibo na duba yiwuwar damar sakin ɗan tawaye Nnamdi Kanu, Shugaba Buhari ya ce “ba za mu iya sakin sa ba”.

Shugaba Buhari yace: “Akwai sashin da ba zan iya taɓawa ba duk da cewa nine a matsayin shugaban kasa saboda yan kasar bazasu yafe min ba, wannan al’amarin na shari’a ba nawa ba. Batun Kanu yana gaban kotu. Amma abin mamakin shi ne, lokacin da yake Turai yana zagin wannan gwamnati, na zaci zai so ya zo qasar domin ya kare kansa daga waɗan nan zarge-zargen da ake masa.

Saboda haka muna ba shi dama ce ta kare kan sa kafin mu aiwatar da abinda ya kamata muyi masa bisa tsarinmu, ba zamu bashi damar komawa kasar waje ba domin ya ci gaba da zaginmu ba, kamar ba ɗan Najeriya ba. Ya zo nan ya soke mu tunda yana ganin kamar yana da wata fawa daze iya kare kansa. waɗanda ke cewa ya kamata a sake shi, a’a, ba zamu iya sakin sa ba amma idan su suna da damar da zasu iya wanke shi su sake shi ga fili nan kuma game doki.”

A wannan watan Nuwamba din daya gabata ne manyan dattawan Nigeria suka gana da Buhari a babban birnin kasar Nigeria wato Abuja, inda suka nemi ya tausaya wa jagoran na haramtacciyar ƙungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) da ke neman kafa ƙasar Biafra a kudu maso gabashin Najeriya wanda mu kuma muka matse shi domin karya samu damar yada ta’addanci a fadin kasar.

A MATSAYINA NA SHUGABA BANA GOYON BAYAN ZABEN ‘YAN TINQE

Shugaban ya ce: ba ya goyon bayan sabon tsarin zaɓe na ‘yar tinƙe yayin zaɓen ‘yan takara da zasu tsaya a shekara me kamawa a matsayin qusoshin gwamnati a cikin jam’iyyun siyasa, wanda sabuwar dokar zaɓe ta tanada.

Shugaba Buhari ya ce ya kamata a bai wa mutanen kasar ‘yan Najeriya zaɓi kala uku su zabi duk wanda suke so a gudanar da zaben dashi, ba wai ‘yar tinqe kawai ba wanda hakan ze jawo cece kuce.

BUHARI YACE BE KAMATA A KIRKIRI WASU SABABBIN ‘YNA SANDAN JAHOHI BA

Shugaba Buhari ya ce: babu wata maganar ƙirƙirar sababbin ‘yan sandan jihohi shidai be aminta ba bada yawunsa bayayin da yake maganar rikicin makiyaya da manoma da suka hadda rashin kwanciyar hankali a kasar sa.

Ya qara da cewa: “Ko a yanzu kun ga gwamnatocin jiha na bai wa ƙananan hukumomi haƙƙinsu?

To wannan shine babban dalilin daya saka bama goyan bayan kirkirar sabbabin yan sandan saboda kaucewa zalinci.

THANK YOU FOR VISITING OUR SITE. WWW.HAUSATALENT.COM

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button